PDP ta yi wa El-Rufai wankin babban bargo a kan tsawaita rufe Kaduna na tsawon kwanaki 30

PDP ta yi wa El-Rufai wankin babban bargo a kan tsawaita rufe Kaduna na tsawon kwanaki 30

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jahar Kaduna, ta caccaki Gwamna Nasir El-Rufai a kan tsawaita dokar hana fita na sa’o’i 24 da ya yi a jahar zuwa tsawon wani wata guda.

Jam’iyyar ta yi zargin cewa abun da ya fi damun gwamnatin jahar shine kudaden shiga da za ta samu daga tarar da wadanda suka saba dokar fitan za su biya.

PDP, yayin da ta ke caccakar tsarin yadda gwamnatin jahar ke bi wajen hana yaduwar annobar ta COVID-19, ta ce gwamnati mai mulki ba ta yi wa al’umma karin haske kan irin nasara da ake samu.

PDP ta yi wa El-Rufai wankin babban bargo a kan tsawaita rufe Kaduna na tsawon kwanaki 30
PDP ta yi wa El-Rufai wankin babban bargo a kan tsawaita rufe Kaduna na tsawon kwanaki 30
Asali: UGC

Hakazalika cewa ba ta sanar masu da shirinta na magance annobar a jahar, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Sakataren labaran jam’iyyar a jahar, Abraham Catoh, a wata sanarwa da ya fitar ya ce lallai, “rufe jahar da aka yi wani hanya ne na samun kudi ba wai kawo karshen lamarin ba.”

Sai dai shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jahar, Emmanuel Jekada, ya bayyana zargin PDP a matsayin mara amfani.

Ya ce rufe jahar da aka yi domin amfanin dukkanin al’umman cikinta ne wanda baya bukatar a siyasantar da shi.

KU KARANTA KUMA: Adadin masu cutar Coronavirus a Kano sun kai 115 bayan samun mutane 38 da suka kamu

A wani labari na daban, mun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje a jiya ya ce jihar na fuskantar babban kalubale sakamakon yadda annobar Covid-19 ke yaduwa. Hakan kuwa na bukatar taimakon gaggawa.

Gwamna Ganduje wanda ya yi jawabi yayin karbar kwamitin yaki da cutar Korona na fadar shugaban kasa a gidan gwamnati, ya ce jihar na cikin wani hali a kan cutar.

Ganduje ya yi bayanin cewa, duk da yawan matakan da aka dauka don hana yaduwar cutar a jihar Kano, har yanzu jihar na fama da wasu al'adu da ke yada cutar.

A yayin jinjinawa shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya bada umarnin rufe jihar gaba daya, gwamnan ya ce da an rufe dukkan kasar ne don samun sakamako mafi kyau, jaridar New Telegraph ta wallafa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel