Annobar Coronavirus ta kashe mutane 3 a jahar Sakkwato – Gwamna Tambuwal
Gwamnan jahar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana mutuwar wasu mutane 3 daga cikin mutane 10 dake dauke da cutar Coronavirus a jahar.
Jaridar Punch ta ruwaito gwamnan ya bayyana haka da tsakar daren Talata, 28 ga watan Afrilu, ta bakin hadiminsa a kan harkokin watsa labaru, Muhammad Bello.
KU KARANTA: Adadin masu cutar Coronavirus a Kano sun kai 115 bayan samun mutane 38 da suka kamu
Sanarwar ta ce: “Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jahar Sakkwato ya sanar da mutuwar mutane 3 a sanadiyyar cutar COVID19, duka mamatan uku suna da tattare da wasu cututtuka dake damunsu kamar ciwon siga, ciwon asma da kuma hawan jini.”
A ranar 19 ga watan Afrilu ne jahar Sakkwato ta fara samun bullar cutar Coronavirus, a ranar 23 ga wata kuma aka samu mutum na biyu, a cikin kwanaki 10, har ta kama mutane 10, ta kashe 3.
A hannu guda, an samu sabbin mutane 38 da suka kamu da cuta annobar Coronavirus mai toshe numfashi a jahar Kano, kamar yadda hukumar kare yaduwar cututtuka, NCDC ta bayyana.
“An samu karin mutane 195 da suka kamu da cutar COVID19 a Najeriya kamar haka 80 – Lagos, 38 – Kano, 15 – Ogun, 15 – Bauchi, 11 – Borno, 10 – Gombe, 9 – Sokoto, 5 – Edo, 5 – Jigawa, 2 – Zamfara, 1 – Rivers, 1 – Enugu, 1 – Delta, 1 – FCT, 1 – Nasarawa.
“Zuwa karfe 11:50 na daren Talata 28 ga watan Afrilu, jimillan masu dauke da cutar a Najeriya sun kai 1532, mutane 255 sun warke yayin da mutane 44 suka rigamu gidan gaskiya.” Inji NCDC.
A wani labarin kuma, hukumar majalisar dinkin duniya dake kula da yawan al’ummar duniya, UNFPA, ta ce za’a samu juna biyu da ba’a shirya daukan su ba guda miliyan 7 a fadin duniya.
Hukumar UNFPA ta bayyana haka ne a ranar Talata yayin da take sanar da hasashen da ta yi game da halin da za’a iya shiga a dalilin dokar hana fita saboda Coronavirus.
UNFPA ta ce idan aka kara watanni 6 a dokar hana fita, za’a samu kimanin mata miliyan 47 a kasashe masu tasowa da ba zasu iya samun hanyoyin da suke bi wajen hana daukan ciki ba.
Saboda haka UNFPA ta tabbatar da cewa sakamakon binciken da ta yi ya nuna mata fiye da miliyan 7 za su iya samun juna biyu sakamakon halin kulle da rashin fita da ake ciki.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng