Kotu ta umarci Atiku da Saraki su biya wata mata miliyoyin kudade a kan zaben 2019

Kotu ta umarci Atiku da Saraki su biya wata mata miliyoyin kudade a kan zaben 2019

Wata babbar kotun tarayya dake zaman ta a jahar Legas ta ci tarar dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2019, Alhaji Atiku Abubakar, naira miliyan 5.

Punch ta ruwaito kotun ta umarci Atiku da shugaban yakin neman zabensa, Bukola Saraki su biya wata mata zambar kudi N5,000,000 saboda amfani da hotonta wajen yakin neman zabe.

KU KARANTA: Yan bindiga sun kai ma Yansanda harin kwantan bauna a Kaduna, sun kashe 1, saura sun jikkata

Uwargida Amuda Adekele, wanda yar kasuwa ce a jahar Legas ta shigar da Atiku kara ne bisa yin amfani da hotonta a yakin neman zabe ba tare da neman izininta ba.

Alkalin kotun, mai sharia Ayokunle Faji ne ya yanke hukuncin, inda ya zayyana wadanda zasu biya kudin kamar haka, Atiku Abubakar, mataimakinsa, Peter Obi da Bukola Saraki.

A cewar Uwargida Amuda ta bayyana kotun cewa ta kunyata sosai sakamakon amfani da hoton ta da Atiku tare da jam’iyyarsa ta PDP suka yi amfani da shi.

“Abokai na da suka ga hoton yayin yakin neman zabe sun bayyana min cewa an mayar da ni tamkar wata mara galihu wanda talauci ya yi ma katutu, matar da ta rasa komai, har ma tana shirin kashe kanta ta huta.” Inji ta.

Kotu ta umarci Atiku da Saraki su biya wata mata miliyoyin kudade a kan zaben 2019
Kotu ta umarci Atiku da Saraki su biya wata mata miliyoyin kudade a kan zaben 2019
Asali: UGC

A watan Disambar 2018 ne tawagar yakin neman zaben Atiku a karkashin jagorancin Bukola Saraki suka dira titin Oyin Jolayemi dake Victoria Island Legas don yi ma Atiku yakin zabe.

A lokacin ne tawagar ta nemi jin ta bakin mazauna unguwar, daga cikinsu har da ita, kuma sun yi ta daukan su hotuna yayin tattaunawar, daga nan kawai sai ta ji ana yayata ta a gari.

Don haka Amuda ta nemi kotun ta tilasta ma Atiku ya biya ta zambar kudi naira miliyan 45 saboda tauye mata hakki da aka yi, amma Alkali Faji ya sassauta musu kudin taran.

A wani labarin kuma, Kungiyar kwadago ta Najeriya ta gargadi gwamnati da ma’aikatu game da dakatar da albashin ma’aikata da sunan Coronavirus, ko kuma zaftare musu albashi.

Shugaban NLC, Ayuba Wabba ne ya sanar da haka a ranar Talata cikin wata sanarwa da ya fitar don tunawa da ranar ma’aikata ta duniya na shekarar 2020.

Wabba ya yi kira ga rassan NLC na kowace jaha da ta yi tirjiya ga duk wani yunkurin gwamnati da ma’aikatu na zaftare albashin ma’aikata,a cewarsa ba yanzu bane lokacin rage albashi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel