Matsalar tsaro: Daruruwan mazauna kauyukan Sokoto sun tsere Nijar

Matsalar tsaro: Daruruwan mazauna kauyukan Sokoto sun tsere Nijar

- Daruruwan jama’a da ke zaune a kauyukan jahar Sokoto sun tsallaka iyakar kasar zuwa cikin Jamhuriyar Nijar

- Sun yi hakan ne domin fakewa bayan da 'yan fashin daji suka fatattake su daga gidajensu

- 'Yan fashin sun shiga kauyukan ne domin gujewa hare-haren da sojojin Najeriya ke kai musu ba kakkautawa a dajin Zurmi na jihar Zamfara

Rahotanni sun kawo cewa daruruwan jama’a da ke zaune a kauyukan jahar Sokoto sun tsallaka iyakar kasar zuwa cikin Jamhuriyar Nijar.

An tattaro cewa sun yi hakan ne domin fakewa bayan da 'yan fashin daji suka fatattake su daga gidajensu.

Matsalar tsaro: Daruruwan mazauna kauyukan Sokoto sun tsere Nijar
Matsalar tsaro: Daruruwan mazauna kauyukan Sokoto sun tsere Nijar
Asali: UGC

Wani kakakin masu kaurar ya bayyana cewa a yanzu 'yan fashin ne ke iko da kauyuka guda tara da ke karamar Hukumar Sabon Birni Gobir na jahar Sokoto, sashin BBC Hausa ta ruwaito.

Bayanai sun nuna cewa 'yan fashin sun shiga kauyukan ne domin gujewa hare-haren da sojojin Najeriya ke kai musu ba kakkautawa a dajin Zurmi na jihar Zamfara mai makwabtaka.

A daren Juma'a, 24 ga watan Afrilu, zuwa wayewar garin ranar ne wasu 'yan bindiga suka kai hari wasu kauyuka a yankin Sabon Birnin Gobir da ke jihar ta Sokoto inda suka kashe akalla mutum biyu, sannan suka jikkata wasu da dama.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Gwamnatin tarayya ta kaddamar da ranar 1 ga watan Mayu a matsayin ranar hutu

A wani labarin kuma, mun ji cewa wasu gungun miyagu yan bindiga sun kashe wani jami’in rundunar Yansandan Najeriya mai mukamin Inspekta a garin Falwaya dake kan hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna.

Yan bindigan sun kai harin kwantan bauna ne a kan wata motar Yansanda dake tafiya da yammacin Litinin, 27 ga watan Afrilu a kan hanyarsu ta zuwa Birnin Gwari.

Wani dan banga dake yankin, Hussaini Imam ya shaida ma Daily Trust cewa jami’in dansandan da aka kashe yana aiki ne a ofishin Yansanda dake Buruku, cikin karamar hukumar Chikun.

Hussaini ya ce yan bindigan sun sake kai wani samame a kauyen Udawa dake karamar hukumar Chikun a ranar Talata, inda suka yi awon gaba da dakacin kauyen.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel