Ba mu da niyyar daga zaben Jihohin Edo da Ondo tukuna – Inji INEC

Ba mu da niyyar daga zaben Jihohin Edo da Ondo tukuna – Inji INEC

Ganin yadda annobar COVID-19 ta tsaida abubuwa cak a Najeriya da sauran kasashen Duniya, hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ta yi magana game da zabukan da za ayi bana.

Hukumar INEC ta musanya rade-radin da ake yi na cewa ta dage zabukan gwamnonin jihohin Ondo da Edo wanda aka tsara za a gudanar a kusa da karshen wannan shekara mai ci 2020.

Jaridar Daily Trust ta rahoto hukumar ta na cewa kawo yanzu ba ta dauki matakin sauya jadawalin zabukan ba. Ana sa ran gudanar da wadannan zabuka ne a Satumba da Oktoba.

Kwamishinan INEC ya ce: “Idan za a tuna, hukumar ta fitar da jadawali da shirin zabukan nan biyu a ranar 6 ga watan Fubariru. Tun daga wancan lokaci zuwa yanzu, ba a taba jadawalin ba."

INEC ta kara da cewa: “Duk da mu na sane da irin ta’adin da cutar Coronavirus ta ke yi, mu na kuma bibiyar kokarin da gwamnatin tarayya da na jihohi da kuma malaman lafiya su ke yi.”

KU KARANTA: Mutum 138 sun murmure tsaf daga cutar COVID-19 a Jihar Legas

Hukumar zaben ta bakin kwamishinan ta nuna cewa gwamnatoci da ma’aikatan asibiti da sauran masu ruwa da tsaki su na bakin kokari na kawo karshen yaduwar wannan cuta.

Mai magana da bakin INEC, Festus Okoye ya ce: “Idan lokaci ya zo kuma akwai bukatar ayi wa jadawalin kwaskwarima, za mu sanar da jama’a kamar dai yadda mu ka saba sanar da su.”

Okoye ya karkare jawabin na sa da cewa: “A daidai wannan lokaci, za mu cigaba da lura da lamarin da kyau tare da hada-kai da masu ta-cewa wajen yaki da annobar COVID-19.”

A cikin watan Satumba da Oktoba masu zuwa ne gwamnonin Edo da Ondo watau Godwin Obaseki da Rotimi Akeredolu za su san matsyarsu. Jam’iyyar APC ce ke mulki a jihohin biyu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng