Covid-19: Abinda FG ta fada a kan bude makarantu

Covid-19: Abinda FG ta fada a kan bude makarantu

Duk da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya sassauta dokar kulle jihohin Abuja, Lagos da Ogun, gwamnatin tarayya ta ce babu ranar bude makarantu.

A daren ranar Litinin ne shugaba Buhari ya gabatar da jawabi kai tsaye ga 'yan Najeriya, inda ya bayyana cewa FG ta fara sassauta dokar rufe jihohin uku.

Kazalika, FG ta ce hukumar shirya jarrabawar kammala makarantun sakandire ta kasashen Africa ta yamma (WAEC) ba ta soke jarrabawar da dalibai za su rubuta ba.

A cewar FG, dalibai za su rubuta jarrabawar WAEC a lokacin da gwamnati ta ga yafi dacewa.

Karamin ministan ilimi na kasa, Emeka Nwajiuba, ne ya bayyana hakan yayin da ya ke amsa tambayoyin manema labarai a wurin taron kwamitin ko ta kwana na kasa a kan annobar covid-19 (PTF).

Ministan ya bayyana cewa babu wata rana ko lokaci da ma'aikatar ilimi ta tsayar domin sake bude makarantu a Najeriya.

Nwajiuba ya ce gwamnatin tarayya ba zata saka rayuwar dalibai a cikin hatsari ba, a saboda haka babu ranar bude makarantu har sai abinda hali ya yi.

Covid-19: Abinda FG ta fada a kan bude makarantu
Emeka Nwajiuba
Asali: UGC

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya rattaba hannu a kan dokokin dakile yaduwar cututtuka ma su yaduwa a jihar Bauchi.

An kirkiri dokokin ne domin kawo karshen yaduwar annobar cutar covid-19 a jihar Bauchi.

"Kafin wannan lokaci, mun saka wasu dokoki da suka hada da takaita zirga - zirga, rufe kasuwanni, haramta achaba, dakatar da taron jama'a da takaita adadin mutanen da babur mai kafa uku da motocin haya za su dauka.

DUBA WANNAN: Annobar mutuwar jama'a: Abinda Ganduje ya fada a kan tallafin da Buhari ya sanar za a bawa Kano

"Mun dauki wadannan matakai domin alhakin kare lafiyar jama'a ya rataya a wuyanmu duk da mun san yin hakan ya takura jama'a. Amma, dole ne mu dauki duk wasu matakai domin rayukan jama'ar jihar Bauchi.

"Wadanda aka samu suna karya dokar zaman gida, kin amfani da takunkumin rufe fuska da 'ma su yin acahaba zasu biya tarar N5,000.

"Ma su karya dokar nesanta zasu biya tarar N5,000, motocin haya, a cikin jihar Bauchi, da basu bi tsarin nesanta ba zasu biya tarar N10,000, yayin da motocin hayar da suka shigo daga wasu jihohin za a ci tararsu N20,000, manyan motocin dako kuma za a ci tararsu N30,000," a cewar gwamnan jihar Bauchi.

A cikin wata sanarwa da gwamnan ya fitar a shafinsa na tuwita, ya ce, dokar, wacce ya rattaba hannu a kanta a yau, Talata, za ta fara aiki ne nan take.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng