‘Yan rawa, da Liman su na cikin mutum 49 da aka kama su na saba dokar kulle
Motoci akalla bakwai dauke da fasinjoji 95 aka kama su na shirin barin Legas a ranar Lahadi. Hakan ya zo ne a lokacin da gwamnati ta haramta zirga-zirga saboda annobar COVID-19.
Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar Legas, Bala Elkana ya shaidawa ‘yan jarida cewa wadannan fasinjoji su na niyyar zuwa garuruwan Benuwai ne da Ilorin da kuma Abuja.
Tuni ‘yan sanda su ka gurfanar da su a kotu domin amsa laifinsu. The Nation ta ce wadannan su na cikin mutane 620 da jami’an ‘yan sanda su ka kama da laifin saba doka a makon jiya.
Daga cikin wadandda aka kama a makon da ya gabata akwai wani limami na masallacin Sheikh da ke unguwar Mile 12 a Ketu watau Sheikh Suleiman Abubakar tare da dinbin mabiyansa.
Wannan limami ya jagoranci sallar Maghriba da Isha’i ne a masallaci a ranar da aka soma azumi. Idan ba ku manta ba gwamnatin jihar Legas ta bada umarnin a rufe duk wani wurin ibada.
KU KARANTA: Buhari ya rufe Kano na makonni biyu, zai aiko kayan yaki da COVID-19
Duk a wannan rana, ‘yan sanda sun yi nasarar cafke wasu ‘yan rawa har mutum 39 a wani otel a unguwar Idimu. Kafin wannan rana an kama wasu mutum 10 da laifin shirya casu a Lekki.
Idan mu ka koma jihar Ondo kuma za mu ji cewa kwamitin da ke yaki da annobar COVID-19 ta kama wasu mutane a gidan mata masu zaman kansu a unguwar Shasha da ke garin Akure.
Mai taimakawa gwamnan Ondo a kai ayyuka na musamman da tsare-tsare, Dr. Doyin Odebowale, ya tabbatar da cafke wadannan mutane da su ka sabawa doka, ya ce yanzu su na killace.
Za a yi wa wadanda aka kama cikin dare a gidan matan gwajin cutar COVID-19 domin a san halin lafiyarsu. Dr. Doyin Odebowale ya ce an kama wadannan mata har su 18 ne a cikin dare.
Odebowale ya ce: “Mun kama su da kusan karfe 10:30 na dare. Mun kawo ma’aikatan lafiya su yi masu gwajin cutar COVID-19. An rufe gidan matan. Za mu gayyaci mai wannan gida.”
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng