Yanzu Yanzu: Gwamnatin tarayya ta kaddamar da ranar 1 ga watan Mayu a matsayin ranar hutu

Yanzu Yanzu: Gwamnatin tarayya ta kaddamar da ranar 1 ga watan Mayu a matsayin ranar hutu

Gwamnatin tarayya ta bayyana ranar Juma’a, 1 ga watan Mayu, a matsayin ranar hutu domin bikin ranar ma’aikata na duniya.

Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Adesoji Aregbesola, ne ya sanar da hakan a madadin gwamnatin tarayya.

A cewar wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren din-din-din na ma’aikatar, Barista Georgina Ehuriah, Aregbesola ya yabawa ma’aikatan Najeriya a kan jajircewarsu, hakuri da kuma fahimta.

Ya yi jinjina ta musamman ga ma’aikata a kan goyon bayan da suke bawa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari a kokarinta na hana yaduwar annobar COVID-19 a fadin kasa.

Yanzu Yanzu: Gwamnatin tarayya ta kaddamar da ranar 1 ga watan Mayu a matsayin ranar hutu
Yanzu Yanzu: Gwamnatin tarayya ta kaddamar da ranar 1 ga watan Mayu a matsayin ranar hutu
Asali: Facebook

Aregbesola, wanda ya ci gaba da godiya ga yan Najeriya da kungiyar kwadago (NLC) a kan sadaukarwarsu a wannan mawuyacin lokaci.

Ya bayar da tabbacin cewa jajircewa da hakurinsu zai taimakawa kokarin gwamnati na tabbatar da dakile yaduwar cutar.

Ya bayyana cewa da irin wannan hadin kai da al’umma ke bayarwa da kuma bin matakan da hukumomi suka shimfida, za a shawo kan matsalolin da yan Najeriya ke fuskanta sakamakon bullar annobar nan ba da jimawa ba.

KU KARANTA KUMA: Majalisa ta amince ma Buhari ya sake antayo ma Najeriya bashin N850,000,000,000

Ministan ya bayar da tabbacin cewa tattalin arzikin Najeriya zai koma daidai har ma kara karfi, duba ga kokarin da gwamnatin tarayya ke yi don daidaita tattalin arzikin.

Daga karshe ya yi kira ga yan Najeriya da su cigaba da hakuri da saka ran samun nasara a kan annobar covid-19.

A wani labarin kuma, mun ji cewa gwamnatin tarayya a ranar Alhamis ta karyata ikirarin da ake yi na cewa ta raba wa jihohin Kudu maso Yamma shinkafar da kwari suka lalata inda ta ce an tabbatar da ingancin kayan abincin.

The Punch ta ruwaito cewa Ministan walwala da jin kai, Sadiya Umar-Farouq, ta ce hukumar kula da ingancin abinci da magunguna na kasa, NAFDAC, ta amince da ingancin shinkafar da aka raba a matsayin tallafi.

Umar Faruq wacce ta yi wannan bayanin yayin jawabi a kan COVID-19 a Abuja ta kuma karyata ikirarin da ake yi na cewa maaikatar ta ta karkatar da kaduden N-Power don sayan kayan tallafin COVID-19.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel