Uba Sani ya yi haramar rabawa dinbin mutane kayan abinci da azumi

Uba Sani ya yi haramar rabawa dinbin mutane kayan abinci da azumi

Masu azumi za su yi murmushi a lokacin da ake tsakiyar fama da annobar cutar COVID-19 a Kaduna. Sanata Uba Sani ya sha alwashin ciyar da dinbin mutane a wannan wata.

Sanatan Kaduna ta tsakiya, Uba Sani ya kaddamar da wani shirin raba kayan abinci a mazabarsa. Sanatan ya na da niyyar ciyar da gidaje miliyan biyu da ke yankin da ya ke wakilta.

Malam Uba Sani ya kaddamar da wannan shiri ne kwanan nan kamar yadda mu ka samu labari daga jaridar The Nation. A ranar Juma’a ne dai musulman Duniya su ka dauki azumi.

Ganin yadda musulmai su ka samu kansu wannan wata a cikin annoba, ‘dan majalisar dattawan ya shirya rabon abinci domin ya ragewa al’ummar yankin tsakiyar jihar Kaduna radadi.

Wannan shiri da sanata Uba Sani ya zo da shi zai amfani mutanen da su ka fito daga cikin kananan hukumomi bakwai na yankin da ‘dan siyasar ya ke wakilta a majalisar dattawa.

KU KARANTA: Sanata Sani ya yi bada gudumuwa ga wadanda wuta ta ci dukiyarsu

“Kayan tallafin sun kunshi abinci kamarsu shinkafa, gero, sukari, man gyara wanda aka warewa gidaje miliyan biyu, kuma za a cigaba da wannan rabo har nan da kwanaki bakwai.”

Sanatan ya ce: “Za a raba kayan tallafin ne ga kungiyoyin addinai, gidajen marayu, kungiyoyin mata, shugabannin gargajiya da kuma kungiyoyin marasa karfi da marasa galihu.”

Sani ya ce a halin yanzu Duniya ta na fama da wannan annoba ta COVID-19. A jawabinsa, ya nuna goyon baya ga matakin da ya zama dole ga gwamnatin Kaduna na garkame jihar.

Rahotanni sun ce darajar wannan kaya da aka zo da su cike da manyan motoci 12 ya kai Naira miliyan 80. Sani ya kuma jagoranci gudumuwar da ‘yan majalisar Kaduna su ka bada.

A lokacin da ya kaddamar da wannan shiri, sanatan na APC ya yi kira ga mutanensa su raba abincin ba tare da la’akari da addini, ko kabila ko kuma jam'iyyar siyasar mutum ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel