COVID-19: Gawar dan sanda ta kawo firgici da tashin hankali
- Rundunar 'yan sandan jihar Imo ta tabbatar da tsintar gawar wani dan sanda mai mukamin sifeta a garin Owerri
- Kamar yadda jaridar Daily Trust ta bayyana, gawar ta tada hankulan jama'ar birnin sakamakon bullar cutar Covid-19 a jihar
- Kamar yadda kakakin 'yan sandan jihar ya tabbatar, duk wadanda suka yi mu'amala da gawar ko kuma suka kusanceta, tilas ne a yi musu gwajin cutar
Tsintar gawar dan sanda da aka yi a garin Owerri ya tada hankulan jama'a a birnin. Hakan ya faru ne a lokacin da ake tsaka da jimamin samun mutum na farko mai dauke da cutar COVID-19 a jihar.
An gano cewa gawar ta wani sifetan 'yan sanda ne kuma an sameta ne gaban sansanin 'yan sanda na Shell wanda ke kallon makarantar firamare ta Alvaina da ke tsakiyar birnin Owerri.
An samu gawar ne da safiyar yau Talata.
Har a halin yanzu dai ba a san dalilin mutuwar mamacin ba amma majiya daga jami'an tsaro ta tabbatar da cewa ana gudun gawar sakamakon cutar Covid-19.
Kamar yadda wakilin jaridar Daily Trust da ya ziyarci wurin ya tabbatar, rundunar masana kiwon lafiya ta 'yan sanda sun je tare da dauke gawar.
KU KARANTA: COVID-19: Sabbin dokokin El-Rufa'i na kullen jihar Kaduna
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Orlando Ikeokwu ya ce duk wadanda suka taba gawar ko suka kusanceta sai an yi musu gwajin cutar Covid-19.
Ya kara da cewa, jami'an 'yan sanda sun fara bincike a kan sanadiyyar mutuwar kuma za su bayyana idan an kammala.
A wani labari na daban, A jiya ne gwamnatin jihar Kaduna ta sake sauya salon bude jihar na kwanaki biyu don siyayya kafin a ci gaba da zaman gida.
Daga yanzu za a dinga bude jihar ne a ranakun Laraba da Asabar don samun damar siyayyar abubuwan bukata.
A wata takarda da ta fito daga mai bada shawara ga gwamnan jihar na musamman a fannin yada labarai, Muyiwa Adekeye, ya ce wannan hukuncin an yanke shi ne bayan taron kwamitin yaki da cutar coronavirus na jihar, wanda mataimakiyar gwamna, Hadiza Balarabe ke shugabanta.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng