Yawan mace-mace: Kano ta sake rasa wani babban jigonta

Yawan mace-mace: Kano ta sake rasa wani babban jigonta

A yayinda ake tsaka da yawan mace-mace na ban al’ajabi a Kano, jahar ta sake rasa wani jigon ta.

Dr Ghali Umar na sashen ilimin fasalin gine-gine a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta jahar Kano, ya rasu a ranar Litinin, inda hakan ya kara rura wutar fargaba da tsoro a birnin.

Shugaban jami’ar, Farfesa Shehu Musa, a cikin wata sanarwa, ya ce: “Muna bakin cikin sanar da mutuwar Arch. Dr. Ghali Kabir Umar, na sashen fasalin gine-gine.”

Har zuwa mutuwarsa, Ghali ya kasance Shugaban sashen gine-gine kuma babban lakcara a bangaren, a jami’ar kimiyya da fasaha ta Kano, da ke Wudil.

Yawan mace-mace: Kano ta sake rasa wani babban jigonta

Yawan mace-mace: Kano ta sake rasa wani babban jigonta
Source: Twitter

Daga nan Musa ya roki Allah ya yafe wa Umar kura-kurensa sannan ya saka masa da Jannatul Firdaus.

Umar ya kasance babban malami na biyar da ya mutu a Kano cikin sa’o’i 72 da suka shude.

A gefe daya mun ji cewa har yanzu rahotanni na cigaba da bayyana yadda ake cigaba da samun yawaitar mutuwar mutane a Kano duk da tabbacin da gwamnati ta bayar na cewa ta shawo kan lamarin.

A ranar Lahadi ne kwamishinan yada labarai a jihar Kano, Muhammad Garba, ya bukaci jama'a su kwantar da hankulansu tare da basu tabbacin cewa nan bada dadewa ba gwamnati za ta warware matsalar.

Mutane da dama sun mutu a cikin mako guda a jihar Kano.

A cewar Sabitu Shaibu, mataimakin shugaban kwamitin ko ta kwana a kan annobar covid-19 a jihar Kano, ya ce adadin mutanen da su ka mutu a Kano ya kai 640, kamar yadda jaridar 'TheCable' ta rawaito.

Wasu na zargin cewa annobar cutar covid-19 ce ke hallaka mutane a Kano.

KU KARANTA KUMA: Majalisar dokokin tarayya ta dawo zama bayan hutun COVID-19

Sai dai, a cewar Garba, mutane na mutuwa ne daga cututtuka irinsu hawan jini, zazzabi, ciwon sukari da sauransu.

Kazalika, mai martaba sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya tabbatar da cewa ba annobar covid-19 ce ke hallaka mutane a masarautarsa ba, kamar yadda wasu su ke zargi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Newspaper

Online view pixel