An samu bullar cutar korona karo na farko a jihar Nasarawa

An samu bullar cutar korona karo na farko a jihar Nasarawa

Rahotanni sun bayyana cewa a karon farko an samu bullar cutar korana a jihar Nasarawa da ke yankin Arewa ta Tsakiya a Najeriya.

Babban jami'in ma'aikatar lafiya na jihar, Dr Ibrahim Adamu, shi ne ya bayar da tabbacin wannan rahoto da jaridar Daily Trust ta ruwaito,

Dr Adamu ya ce tuni aka killace wadda aka gano tana dauke da kwayoyin cutar bayan da sakamakon gwajinta ya tabbatar da hakan.

Wani abun mamaki shi ne yadda sai a yanzu bayan da aka shafe tsawon makonni ba tare da bullar cutar a jihar Nasarawa ba duk da kusancinta da babban birnin tarayya.

Gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule ya ce wata matashiya ce ke dauke da cutar wacce ta fito daga Kano a makon da ya gabata duk da matakan hana fita da gwamnatin ta dauka.

A halin yanzu akwai fiye da mutane da 100 da cutar korona ta harba a garin Abuja.

A daren ranar Litinin, cibiyar dakile cututtuka masu yaduwa a kasar, NCDC, ta sanar da samun karin mutane 64 da suka kamu da cutar korona a fadin kasar.

Gwajin cutar korona
Gwajin cutar korona
Asali: UGC

Ya zuwa yanzu dai mutum 1337 ne suka kamu da cutar korona a duk fadin Najeriya kamar yadda NCDC ta sanar kan shafinta na Twitter da misalin karfe 11.20 na daren 27 ga watan Afrilu.

KARANTA KUMA: Cutar korona ta hallaka mutane 2 a jihar Kano

Alkaluman da NCDC ta fitar a ranar Litinin sun nuna cewa an samu raguwar adadin sabbin mutane wadanda cutar korona ta harba idan an kwatanta da alkulaman baya.

Taskar bayanai ta NCDC ta nuna cewa an samu karin mutum 34 da cutar ta harba a jihar Legas, 15 a Abuja, 11 a Borno, sai kuma mutum biyu a kowane daya daga cikin jihohin Taraba da Gombe.

Haka kuma mutane 255 ne suka warke yayin da tuni mutum 40 suka riga mu gidan gaskiya bayan kamuwa da cutar a duk fadin kasar.

A jiya ne ma'aikatar lafiya ta jihar Kano ta sanar da mutuwar karin wasu mutum biyu da cutar korona ta harba a jihar. A yanzu mutum uku kenan cutar ta hallaka a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng