Diyar Abba Kyari ta fada ma magauta su rabu da babanta ya kwanta cikin aminci

Diyar Abba Kyari ta fada ma magauta su rabu da babanta ya kwanta cikin aminci

Daya daga cikin yaran marigayi shugaban ma’aikatan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Mallam Abba Kyari mai suna Aisha, ta bukaci masu suka da su bar ruhin mahaifinta ya huta.

Ta bayyana hakan ne a shafinta na Instagram a jiya Litinin, 26 ga watan Afrilu, jaridar Thisday ta ruwaito.

Aisha, wacce ta yi martani a shafinta mai suna crackeddiamond, ta kuma caccaki wasu mutane wadanda ta zarga da tambayan inda mahaifinta ya shiga.

Diyar Abba Kyari ta fada ma magauta su rabu da babanta ya kwanta cikin aminci

Diyar Abba Kyari ta fada ma magauta su rabu da babanta ya kwanta cikin aminci
Source: Facebook

“Mahaifina, Abba Kyari ya tafi. Har yanzu mugaye ba za su yi shiru ba. Dukkanin ku da kuke ikirarin shine tushen matsalolinku a lokacin da yake raye, toh yanzu babu shi, shakka babu dukkanin matsalolinku ya mutu tare da shi. Ku barmu mu da muke son sa mu yi jimaminsa cikin aminci.

“Sannan ya kai Lola Omotayo da sauran ku da kuke son sanin inda yake, ina fatan yanzu da kuka san inda yake, kuna bacci da kyau da daddare," cewar Aisha.

KU KARANTA KUMA: Covid-19: Mutane fiye da 100 sun mutu bayan sun sha wani jikon maganin gargajiya

A wani labarin kuma, mun ji cewa gamayyar wasu kungiyoyin goyon bayan shugaban kasa, Muhammadu Buhari, sun yi kira gare shi da ya nada Injiniya Kilani Mohammed a gurbin marigayi Abba Kyari.

Gamayyar kungiyoyin a karkashin inuwar PBS sun bayyana cewa akwai bukatar Buhari ya samu gogaggen dan siyasa da ya san aiki domin nada shi a gurbin da marigayi Kyari ya bari.

Kungiyoyin PBS sun yi wa Buhari nemanyakin zabe tun farkon shigowarsa siyasa a 2003. Sune su ka fara kirkiro salon kare kuri'un da aka jefawa Buhari a karkashin tsarin 'A kasa A tsare'.

A karshen makon jiya ne marigayi Abba Kyari ya mutu a wani asibiti da ke jihar Legas, inda aka kwantar da shi bayan an tabbatar da cewa ya na dauke da kwayar cutar covid-19.

Tun bayan mutuwarsa rahotanni su ka fara bayyana jerin wasu manyan 'yan arewa ma su kusanci da shugaban kasa da ke zawarcin kujerarsa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel