COVID-19: An sake sallamar mutanen da su ka warke a dakunan Legas

COVID-19: An sake sallamar mutanen da su ka warke a dakunan Legas

A halin yanzu ana cigaba da warkewa daga cutar COVID-19 a Najeriya. A farkon makon nan aka bada sanarwar cewa wasu wadanda ke dauke da wannan cuta sun samu sauki a Legas.

Gwamnatin jihar Legas ce ta bada wannan sanarwa a jiya ranar Litinim, 27 ga watan Afrilu, 2020. Gwamnatin ta bada wannan sanarwa ne ta dandalin shafin sada zumuntanta na Tuwita.

Mutane 15 ne su ka samu lafiya a Legas a cikin makon nan, kuma tuni aka sallamesu zuwa gida. Daga cikin wadanda su ka warke har da wani Bawan Allah da ya fito daga kasar Indiya.

Sanarwar ta ce: “An sake samun mutane 15 da ke jinyar cutar COVID-19 a Legas da su ka samu sauki; daga ciki akwai mata 11 da maza 4, har da wani mutumin kasar waje – Ba’Indiye.”

Jawabin sallamar da ya fito daga ma’aikatar lafiyar Legas ya kara da cewa: “An sallame su daga dakin killace marasa lafiya da ke Yaba da Onikan, za su koma cikin sauran al’umma.”

KU KARANTA: Sakamako ya fito bayan tsohon Gwamna Tinubu ya yi gwajin COVID-19

“Mutum 11 sun samu sauki ne a asibitin kula cututtuka masu yaduwa da ke garin Yaba, 4 sun warke ne daga dakin killace mutane na Onikan. Dukkaninsu sun saumu lafiya.” Inji jihar.

Gwamnatin Babajide Sanwo-Olu ta tabbatar da cewa an yi wa wadannan Bayin Allah gwaji sau biyu, kuma sakamako ya nuna babu shakka kwayar wannan cutar COVID-19 ta bar jikinsu.

Ma’aikatar lafiyar ta ce: “Da wannan sallama da aka yi, wadanda su ka warke daga cutar COVID-19 a Legas ya kai 138.” NCDC ta ce mutane 255 su ka samu sauki daga cutar a fadin Najeriya.

A jiya ana da mutane 764 da su ke dauke da wannan cuta a Legas. Wannan ya nuna cewa 57% na wadanda su ka kamu da cutar su na wannan jihar inda kusan 20% su ka samu lafiya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel