Enahire: A fito da binciken abin da ke kashe mutane a Jihar Kano – Falana

Enahire: A fito da binciken abin da ke kashe mutane a Jihar Kano – Falana

A yanzu ana fama da yawan mace-mace a jihar Kano, inda daruruwan mutane su ke mutuwa a kowane mako. Wannan ya sa gwamnati ta fito ta bayyana cewa za ta gudanar da bincike.

Babban lauyan nan mai kare hakkin ‘dan Adam, Femi Falana SAN, ya bukaci ministan lafiya Dr. Osagie Ehanire ya fito da rahoton binciken da gwamnatin tarayya da jihar Kano su ka gudanar.

Femi Falana SAN wanda shi ne shugaban rikon kwarya na wata kungiya mai lura da kokarin da ake yi wajen yaki da cutar COVID-19 a Najeriya, ya shaida wannan a wata wasika da ya fitar.

Falana ya rubutawa ma’aikatar lafiya takarda, ya na neman mai girma minista Osagie Ehanire ya fito da cikakken rahoton binciken da aka yi. Lauyan ya ba ministan mako guda ne ya yi wannan.

Falana SAN ya ce idan aka zarce wannan lokaci ba tare da an fitar da rahoton ba, zai kai gwamnati kotu domin shari’a ta yi halinta. Zai sa a tursasawa gwamnati ta fito da wannan rahoto.

KU KARANTA: An sake samun Mutane 64 da su ka harbu da cutar COVID-19 - NCDC

Enahire: A fito da binciken abin da ke kashe mutane a Jihar Kano – Falana

Falana ya na so a fadi abin da ya jawo mace-mace a Kano
Source: UGC

Wannan lauya da ya yi fice ya dogara ne da dokar FOI wanda ta ba shi damar samun duk wani bayani daga gwamnatin kasar. Wasikar ta shiga hannun ministan a karshen makon da ya wuce.

Rahotanni daga TVC sun bayyana cewa wannan kungiya ta su Femi Falana ta bukaci a bayyana masu abin da aka gano a binciken da aka yi game da yawan mace-macen da ake yi a jihar Kano.

“Rahoton ya kunshi sila da yanayin mutuwar da ake yi, da adadin wadanda su ka mutu da kuma wadanda su ke jinya a asibitoci, tare da matakan da gwamnatin tarayya ta dauka.” Inji Lauyan.

Bayan haka, kungiyar ta bukaci gwamnatin tarayya ta karbi ragamar shawo kan halin da aka shiga a Kano. Falana da kungiyarsa sun ce lamarin da aka shiga ya fi karfin gwamnatin jihar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel