Legas: Gobara ta barke a wani gidan man NNPC a Unguwar Ogba
A yau Litinin, 27 ga watan Afrilu, 2020, aka gamu da wata babbar musiba ta gobara a jihar Legas. Wannan gobara ta barke ne a lokacin da jihar ta ke fama da annobar cutar COVID-19.
Gidan man kamfanin NNPC da ke yankin Yaya Abatan a unguwar Ogba da ke jihar Legas ne ya kama ci da wuta a yau da rana. Jaridar The Nation ta rahoto wannan mummunan labari.
Wannan gobara da ta kama a kan titin College Road ta ci wasu gidaje da ke kusa da gidan man. Har zuwa lokacin da mu ka samu wannan rahoto, ba a san me ya jawo wannan wuta ba.
Rahotanni sun bayyana cewa jami’ai sun sha wuya wajen kashe wannan wuta. Wasu mutane sun dauki bidiyo yayin da wannan wuta ta ke cigaba da ci a gidan man na kamfanin NNPC.
Akalla gidaje biyar su ka kama da wuta a sanadiyyar wannan gobara da ta taso daga gidan man. Wannan ya sa jama’a su ka yi carko-carko su ka rasa inda za su shiga domin su tsira.
KU KARANTA: Wuta ta ci Mai jero, da jariri da wasu mutum 3 a Kaduna
Daga baya ma’aikatan kwana-kwana sun yi kokarin kashe wutar. Mutanen da ke kusa sun kawo agaji inda aka hangi wasu mutanen Legas su na yunkurin kashe gobarar da ruwan leda.
Wani mutumi wanda wutar ta fara ci a gabansa mai suna Nosa Gabriel ya shaidawa ‘yan jarida cewa ‘yan kwana-kwana sun yi zuwan banza, domin su zo wurin ne da mota ba tare da ruwa ba.
Mista Nosa Gabriel ya tabbatar da cewa wata mota da ke kusa da gidan man ta kone kurmus a sanadiyyar wannan gobara. Legit.ng ba ta da labarin adadin dukiyar da aka yi asara a gobarar.
A dalilin wannan gobara dai, jama’a sun sabawa dokar tazara da gwamnati ta kafa. Gwamnati ta ce dole jama’a su guji cinkoso domin gudun kamuwa da muguwar cutar nan ta Coronavirus.
Kwanakin baya an samu irin wannan gobara a garin Kano inda wuta ta ci gidan man Aliko da ke cikin gari. Gobarar ta barke ne a gidan man da ke kan titin Maiduguri cikin tsakiyar dare.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng