Mun sakarwa shugabannin Boko Haram bama-bamai yayin da suke taro a jihar Borno - DHQ

Mun sakarwa shugabannin Boko Haram bama-bamai yayin da suke taro a jihar Borno - DHQ

Jiragen yakin sojojin rundunar atisayen 'Ofireshon Lafiya Dole' sun kashe wasu shugabannin kungiyar Boko Haram yayin da suke wani taro a Kolloram da ke daura da tekun Chadi a jihar Borno.

A sanarwar da hedikwatar rundunar tsaro (DHQ) ta fitar, ta bayyana cewa an kaiwa shugannin kungiyar harin ne bayan samun sahihan bayanai a kan taron da suka shirya domin tsara kai wasu hare-hare.

Sashen watsa labarai na rundunar sojin Najeriya ya fitar da sanarwar cewa an yi wa mayakan kungiyar Boko Haram luguden bama - bamai a ranar Asabar.

Sanarwar ta bayyana cewa rundunar soji za ta cigaba da kai zafafan hare - hare a mafaka da wuraren haduwar mayakan kungiyar Boko Haram da na ISWAP a gefen tekun Chadi.

A cikin sanarwar, manjo janar John Enenche ya ce, "dakarun soji za su cigaba da kai hare - hare a kan 'yan ta'adda a yankin arewa maso gabas.

"A cigaba da kai irin wadannan hare - hare ne rundunar soji ta kaddamar da wani babban hari da jiragenta na yaki a kan 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram da ISWAP a Kolloram.

"Mayakan kungiyoyin da dama sun mutu sakamakon ruwan wuta da bama - baman da sojoji suka sakar musu."

A ranar 20 ga watan Afrilu ne rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun kashe mayakan kungiyar Boko Haram fiye da 100 a kauyen Buni Gari da ke karkashin karamar hukumar Gujba a jihar Yobe.

Mun sakarwa shugabannin Boko Haram bama-bamai yayin da suke taro a jihar Borno - DHQ
Mun sakarwa shugabannin Boko Haram bama-bamai yayin da suke taro a jihar Borno - DHQ
Asali: Twitter

A wani jawabi da kakakin rundunar soji, Kanal Sagir Musa, ya fitar a Damaturu, ya ce an kashe mayakan kungiyar Boko Haram yayin da su ke shirin kaddamar da wani babban hari a kauyen.

Kauyen Buni Gari bashi da nisa daga wata makarantar rundunar soji da ke Bunu Yadi, wacce kuma kuma aka jibge rundunar soji ta musamman domin yaki da 'yan ta'adda a jihar Yobe.

DUBA WANNAN: Mutum biyu sun yi layar zana a jihar Borno bayan sakamakon gwaji ya nuna suna da covid-19

Kanal Musa ya ce dakarun soji a karkashin jagorancin, Janar Lawrence Araba, sun samu nasarar cimma mayakan kafin su kaddamar da harin da su ka shirya kaiwa.

Ya bayyana cewa dakarun soji sun samu sahihan bayanan sirri a kan shirin mayakan na kai hari kauyen ranar Asabar.

Da ya ke nuna wa babban hafsan rundunar sojin kasa, Janar Tukur Buratai, irin makaman da aka samu a wurin mayakan da aka kashe, Janar Araba, ya ce an kashe mayakan Boko Haram 105.

A jawabinsa, Buratai ya yabawa sojoji kafin daga bisani ya wuce zuwa sansanin sojoji na Damaturu domin duba sojojin da su ka samu raunuka yayin gumurzun da su ka yi mayakan Boko Haram.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel