Jihohi 33 a Najeriya wanda cutar Coronavirus ta bulla - NCDC

Jihohi 33 a Najeriya wanda cutar Coronavirus ta bulla - NCDC

Likafar annobar cutar korona na ci gaba a Najeriya duk da irin kai komo da mahukuntan lafiya ke yi babu dare babu rana domin dakile yaduwar cutar a kasar.

A halin yanzu an samu bullar cutar korona a jihohi 33 na Najeriya ciki har da babban birnin tarayya kamar yadda alkaluman cibiyar dakile yaduwar cututtuka a kasar NCDC suka tabbatar.

Taskar bayanai ta NCDC a ranar Lahadi 26 ga watan Afrilun 2020, ta ce cutar corona ta harbi mutane 1273 yayin da tuni mutum 239 suka warke.

Ya zuwa yanzu dai mutane 40 cutar ta hallaka a fadin Najeriya kamar yadda kididdigar alkaluman ta tabbatar.

Ga jerin adadin mutanen da suka kamu da cutar a kowace daya daga cikin jihohi 25 na Najeriya da cutar ta bulla:

Lagos-731; Abuja-141; Kano-77; Ogun-35; Gombe-35; Osun-34; Katsina-30; Borno-30; Edo-25; Oyo-21; Kaduna-15; Bauchi-14; Akwa Ibom-12; Kwara-11; Sokoto-10; Ekiti-8; Ondo-8; Rivers-6; Delta-6; Taraba-6; Jigawa-2; Enugu-2; Niger-2; Abia-2; Zamfara-2; Benue-1; Anambra-1; Adamawa-1; Plateau-1; Imo-1; Bayelsa-1; Ebonyi-1; Kebbi-1.

Da misalin karfe 11.50 na daren ranar Lahadi, cibiyar mai fafutikar dakile yaduwar cututtuka ta sanar da cewa an samu karin mutane 91 da cutar covid-19 ta harba a fadin Najeriya.

An samu karin mutum 91 ne daga jihohi 16 na kasar da suka hadar da; Legas (43), Sokoto (8), Taraba (6), Kaduna(5), Gombe (5), Ondo (3), Abuja (3), Edo (3), Oyo (3), Rivers (3), Bauchi (3), Osun (2), Akwa Ibom (1), Bayelsa (1), Ebonyi (1) da kuma Kebbi (1).

KARANTA KUMA: Coronavirus: An kamo mutumin da ya gudu daga cibiyar killacewa a Borno

Jihohin Najeriya da cutar ta bulla karo na farko a baya-bayan nan sun kasance Ebonyi a yankin Kudu maso Gabas, Bayelsa a yankin Kudancin Kudu, Kebbi a yankin Arewa maso Yamma da kuma Taraba a yankin Arewa ta Tsakiya.

Har ila yau dai jihar Legas ce a kan sahu na gaba ta fuskar yawan wadanda cutar ta kama inda adadinsu ya kai 731, sai kuma birnin tarayya inda cutar ta harbi mutum 141 yayin da jihar Kano ta biyo baya da mutum 77.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Tags: