Ina jin karin farin ciki da cikar buri bayan da na koma addinin Islama – Jarumar wasar kudu
Fitacciyar jarumar wasannin Najeriya, Adunni Ade ta ba mabiyanta mamaki a shafin soshiyal midiya, bayan ta fito ta yi magana a kan wani bangare na rayuwarta.
Jarumar ta bayyana cewa tun da dadewa ta daina yin sharhi a kan abun da ya shafi addini, saboda abune mai matukar kaifi a gare ta. Ta kara da cewa makusantan ta na dab-da-dab ne kadai suka san wani addini ta ke yi.
Hakan ya biyo bayan fitowa da jarumar ta yi domin ta yi Karin haske a kan kokwanton masu rade-radi, sannan ta bayyana cewa ita Musulma ce ta hakika.
Adunni ta bayyana cewa an haife ta a gidan Musulunci sannan an tayar da ita a kan tafarkin addinin Islama.
“Don haka ga wadanda ke ta tambaya, Eh ni Musulma ce. An haife ni a gidan Musulunci sannan an rene ni a kan tafarkin Islama. Idan kuna son sani, B2 na samu a jarrabawar WAEC.
"Mahaifina Musulmi ne wanda ke ba yaransa damar zabar duk addinin da suke so imma na Kirista ko Islama.
"Mahaifiyata Kirista ce, koda dai bata aiki da shi. Kishiyar mahaifiyata ma Kirista ce, yan uwana mata Kiristoci ne, yan uwana maza Musulmai ne,” jarumar ta rubuta.
Da ta ke ci gaba da bayani, Adunni ta bayyana cewa a wani mataki da ta kai a rayuwarta sai ta koma addininin Krista inda ta ke bauta a MFM, RCCG, CLAM, CAC, da sauran cocina.
Ta bayyana cewa yayinda ta ke duk wannan, addinin Islama bai bar jikinta ba.
Adduni ta ce tsawon wasu shekaru tana damuwa a kan abun da mutane za su ce idan ta koma Musulunci. Sai dai kuma, a watan Disamba 2016, sai ta koma addinin Islama.
Ta ce: “Bayan kimanin shekaru 4, a ranar 31 ga watan Disamba 2016, sai na yanke shawarar tafiyar da rayuwata yadda nake so. Na dawo addinin Islama. Na ji muradina ya cika. Na fi jin farin ciki. Sai na fara ganin karin falala. Babban dana Musulmi ne, yana sallah da azumi."
Kan yanayin shigarta, jarumar ta bayyana cewa tana da ikon sanya irin tufafin da ta ga dama saboda addinin Islama na aiki da zuciyar mutum ne.
KU KARANTA KUMA: Mutuwar mutane: Lamarin ya na bani tsoro, FG ta yi watsi da Kano - Ganduje ya magantu
Ta kara da cewa tana son sanar da mutane su yi rayuwa yadda suke so ba tare da la’akari da abun da mutane za su ce a kan su ba.
Daga karshe, jarumar ta yi kira ga Musulmai da su yi amfani da watan Ramadana yadda ya kamata.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng