Coronavirus: An kamo mutumin da ya gudu daga cibiyar killacewa a Borno

Coronavirus: An kamo mutumin da ya gudu daga cibiyar killacewa a Borno

Gwamnatin jihar Borno, ta ce ta samu nasarar cafke mutum daya daga cikin mutane biyun da suka tsere bayan gwaji ya tabbatar da sun harbu da cutar corona.

A rahoton da jaridar The Cable ta wallafa, gwamnatin ta ce ta gano Abbas Kaka Hassan, matashin mai shekaru 24 wanda ya tsere bayan gwaji ya tabbatar da yana dauke da kwayoyin cutar covid-19.

Hassan da Hauwa Muhammad, mai shekaru 42, su ne mutane biyun da suka tsere daga Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri bayan fitowar sakamakon gwajinsu a ranar Lahadin da ta gabata.

Kwamishinan lafiya na jihar Dr. Salisu Kwayabura ya ce an gano matashin ne da misalin karfe 2 na daren Litinin a birnin Maiduguri.

Tun a ranar Lahadin ne mahukuntan lafiya ajihar suka bayar da sanarwa farautar mutanen biyu masu dauke da cutar korona da suka tsere bayan an killace su.

Kwamitin ko ta kwana da gwamnatin jihar Borno ta kafa domin yaki da annobar korona ya bukaci mazauna Maiduguri su ankara a yayin da wasu ma su dauke da kwayar cutar suka tsere.

Gwamnan Jihar Borno; Babagana Umara Zulum

Gwamnan Jihar Borno; Babagana Umara Zulum
Source: Twitter

Kwamishinan ya ce bayan baza tawagar jami'an lafiya da kuma 'yan sanda, an gano mara lafiyan cikin mawuyacin hali a gidansu da ke unguwar Gwanje.

Nan take aka dauke shi cikin gadon daukan marasa lafiya zuwa cibiyar da ake killace wadanda cutar korona ta harba.

KARANTA KUMA: Yawan mace-mace ya jefa al'ummar Kano cikin firgici

Ya zuwa yanzu ba a gano daya matar ba wadda ta kasance mazauniyar gundumar Shuwari da ta tsere bayan gwaji ya tabbatar da tana dauke da kwayoyin cutar korona.

Sai dai an baza jami'ai domin su ci gaba da farautar wannan mata kamar yadda kwamishinan ya bayar da shaida.

A ranar Lahadi, 26 ga Afrilu, taskar bayanai mai fidda alkaluman hukumar dakile yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta tabbatar, an samu mutum 30 da cutar korona ta harba a jihar Borno.

A wani rahoton mai nasaba da wannan da jaridar Legit.ng ta ruwaito, an damke wata mata mai dauke da cutar korona wadda ta tsere daga cibiyar killacewa a Abuja yayin da ta tunkari jihar Nasarawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel