Coronavirus: An hukunta wasu limami 3 da fastoci 2 a Abuja saboda karya doka

Coronavirus: An hukunta wasu limami 3 da fastoci 2 a Abuja saboda karya doka

Hukumomi a babban birnin tarayya Abuja, sun hukunta wasu limaman masallatai da fastocin da suka karya dokar hana taron jama’a.

A bisa ga wani rubutu da bidiyo da hukumar birnin tarayya ta wallafa a shafinta na Twitter ta ce: “An kama limaman su uku da aka samu suna jagorantar Sallar jam’i a masallatai da kuma fastoci biyu da aka samu sun tara jama’a a coci.”

Har ila yau sanarwar ya nuna cewa an yake wa dukkaninsu hukuncin daurin wata daya a gidan yari kan saba dokar hana fita da aka kafa.

An dai sanya dokar hana fita ne a babban birnin da wasu jihohin kasar, a kokari da gwamnatin tarayya ke yi na dakile yaduwar annobar COVID-19.

Hoton bidiyon ya nuna yadda limaman ke jagorantar Sallar jam'i ba tare da mabiyan sun bayar da tazara ba.

Ga bidiyon a kasa:

KU KARANTA KUMA: Mutuwar mutane: Lamarin ya na bani tsoro, FG ta yi watsi da Kano - Ganduje ya magantu

A wani labarin kuma, mun ji cewa Gwamna Dave Umahi ya bayyana cewa ba zai rufe jiharsa tsaf ba duk da halin da aka shiga ciki a Najeriya. A halin yanzu dai akwai dokar hana fita da sassafe da kuma yamma a jihar.

Gwamnatin Ebonyi ta dauki matakin haramta zirga-zirga a wasu lokutan rana domin takaita yaduwar cutar COVID-19. Gwamnatin ta ce ba za ta dauki matakin da ya wuce wannan ba.

Dave Umahi ya ce ba zai garkame jihar gaba daya ba, Umahi ya yi magana ranar Lahadi, inda ya ce ya tsaya ya yi la’akari da yanayin karfin tattalin jihar Ebonyi kafin ya dauki wannan mataki.

“Na yi la’akari da alkaluman talaucin jihar Ebonyi, don haka na ke kira ga masu bada shawarar a rufe dukkanin kasuwanni da su sake duba wannan magana da su ka kawo.” Inji Umahi.

“Ba mu da wanda ya kamu da cutar COVID-19, a dalilin haka babu bukatar rufe hanyoyin neman kudin mutanenmu.”

Mai girma gwaman ya yi wannan jawabi ne jiya a garin Abakaliki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel