Coronavirus: Rabiu Kwankwaso ya aikawa Shugaban kasa Buhari takardar musamman

Coronavirus: Rabiu Kwankwaso ya aikawa Shugaban kasa Buhari takardar musamman

Ganin irin mace-macen da ake yi a Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya aika wasika zuwa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya na rokon gwamnatin tarayyarsa ta kawowa jihar dauki.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi wa wannan wasika ta sa da taken: “COVID-19 da yawan mace-mace masu ban mamaki a Kano: kira ga gwamnatin tarayya ta dauki matakin gaggawa.”

A wasikar, Rabiu Musa Kwankwaso ya bukaci gwamnatin tarayya ta yi maza ta ceci rayukan mutanen jihar Kano. Ana zargi mutum akalla 600 su ka mutu a Kano cikin makon da ya gabata.

Tsohon Sanatan na Kano ya fara da yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari ta’aziyyar Malam Abba Kyari. Haka zalika ya yi wa wadanda su ka kamu da cutar a kasar addu’ar samun sauki.

Kwankwaso ya bayyana dalilai biyar da su ka sa ya rubuta wannan wasika; Daga ciki ya ce akwai yawan mace-macen Bayin Allah da ake samu a jihar, don haka ya ga ya dace ya bada shawara.

Sanata Kwankwaso ya kuma zargi gwamnatin jihar Kano da nuna rashin tsari wajen yaki da annobar COVID-19 a matsayin wani dalili da ya sa ya rubuta wasika zuwa ga shugaban kasa.

Haka zalika fitaccen ‘dan siyasar kasar ya ce akwai rashin hadin-kai tsakanin gwamnatin tarayya da ta Kano, gami da kuma tabarbarewar sha’anin harkar kiwon lafiya a fadin Najeriya.

KU KARANTA: Gwamna Ganduje ya yarda ana fama da ruwan mace-mace a Jihar Kano

‘Dan siyasar ya koka da irin yadda jama’a ke mutuwa, ya ce: “An yi jana’izar daruruwan mutane a makabartun da ake da su a cikin garuruwan birnin Kano a ‘yan makonnin bayan nan.”

Injiniya Kwankwaso ya ce su na zargin akwai laifin gazawar yin gwajin kwayar cutar COVID-19 wajen mutuwar wadannan mutane, tare da nuna tsoron hakan na iya cigaba da aukuwa.

“A halin yanzu babu wani tsayayyen kwamiti mai yaki da cutar COVID-19 a Kano. Abin da mu ka kasance mu na da shi taron wasu wadanda ba su san aiki ba ne kuma ba su cancanta ba.”

“Kwamitin ya wargaza kansa da ‘ya ‘yansa su ka harbu da COVID-19. Zan sanar da shugaban kasa tun lokacin da aka gano cutar ta kama ‘yan kwamitin ba a sake yi wa wani gwaji a jihar ba.”

Injiniya Kwankwaso ya kuma ce gwamnati ta na fama da rashin yardar jama’a, inda ya ce a irin wannan lokaci ana bukatar hadin kai ne, akasin sabanin da ake samu da hukumar NCDC a jihar.

A wasikar ta sa, Kwankwaso ya bada shawarar gwamnatin tarayya ta ceci al’ummar jihar mai dinbin jama’a, sannan ya bukaci a tursasawa gwamatin Kano ta kafa kwamitin kirki a jihar.

Bugu da kari, Rabiu Kwankwaso ya yi kira ga gwamnati ta bude wuraren gwaji akalla 5 a jihar, bayan dakunan karbar jini guda 10, sannan a binciki musababbin mutuwar dattawa a Kano.

Tsohon sanatan ya bada wasu shawarwari da su ka hada da gano wadanda su ka halarci jana’izar wadanda su ka mutu kwanan nan, domin a killacesu sannan ayi masu gwajin cutar COVID-19.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel