Covid-19: Ministan lafiya ya sanar da lokacin da cibiyar gwaji za ta dawo aiki a Kano

Covid-19: Ministan lafiya ya sanar da lokacin da cibiyar gwaji za ta dawo aiki a Kano

Cibiyar gwajin COVID-19 na hukumar kula da hana yaduwar cututtuka ta Najeriya (NCDC) da ke Kano, za ta koma aiki a ranar Litinin, wani jami’in hukumar ya bayyana.

Ministan lafiya, Osagie Ehanire, ya bayyana hakan a ranar Lahadi, 26 ga watan Afrilu, a lokacin wata hira da talabijin din Channels na Sunday Politics, wacce ta mayar da hankali a kan annobar COVID-19 a Najeriya.

Ehanire ya ce: “cibiyar gwajin za ta dawo aiki a gobe (Litinin) saboda tawagarmu sun tafi can daga hukumar NCDC. Mafi akasarinsu sun isa can a yau (Lahadi). Kuma ya kamata su fara tantancewa a gobe (Litinin).

Covid-19: Ministan lafiya ya sanar da lokacin da cibiyar gwaji za ta dawo aiki a Kano

Covid-19: Ministan lafiya ya sanar da lokacin da cibiyar gwaji za ta dawo aiki a Kano
Source: UGC

Da yake magana a kan mace-macen ban mamaki a Kano, ministan ya yi bayanin cewa an tura wata tawaga jahar “domin su yi bincike da kyau a kana bun da ke tattare da rasa rayuka da ake yi a can.”

“Yanayin mutuwar da wakana a can bai yi kama da abun da zai daidaita na dan wani lokaci ba. Amma binciken hukumar zai taimaka mana wajen gano menene ainahin lamarin. Ba a gane ko lamarin na da alaka da coronavirus ba.

“Muna tafiyar da shi a matsayin lamari na musamman, sannan muna duba a kan matakai da kuma ainahin abun da ke faruwa. Kano ba ta da gogewa sosai a harkar coronavirus wacce a yanzu ta bazu, wannan abun damuwa ne."

A baya dai mun ji cewa babban jami'i na kasa kan yaki da cutar corona a Kano, Dr. Aliyu Sani ya ce suna aiki da gwamnatin jahar kan yunkurin shawo kan cutar.

KU KARANTA KUMA: Abdulsamad ya sake bayar da tallafin fiye da biliyan uku don yaki da annobar covid-19

Ya ce dole ce ta sa aka rufe dakin gwajin cutar kwaya daya a Kano, saboda uku daga cikin ma'aikatan da ke gwajin sun kamu da cutar, sannan an killace sauran duka ma'aikatan.

Dr. Aliyu Sani ya ce an yi wa dakin gwajin feshin kashe kwayoyin cuta, kuma dole ne a bar dakin zuwa wasu kwanaki kafin a ci gaba da aiki a cikinsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel