Matashi dan shekara 37 ya kashe mahaifinsa dan shekara 70 a jahar Anambra

Matashi dan shekara 37 ya kashe mahaifinsa dan shekara 70 a jahar Anambra

Wani matashi dan shekara 37, da ake tunanin yana da tabin hankali, Chigorom Ezeofor ya kashe mahaifinsa har lahira da gatari a jahar Anambra.

Jaridar Punch ta ruwaito lamarin ya faru ne a ranar Asabar, 25 ga watan Afrilu a kauyen Umuchiana dake cikin karamar hukumar Aguata na jahar.

KU KARANTA: Da dumi dumi: An sallami mutane 10 da suka warke daga cutar Coronavirus a Legas

Sai dai wasu yan mamacin sun bayyana cewa tun kafin Chigorom ya kashe babansa ya dan kwana biyu yana nuna wasu irin sabbin halayya da basu san shi da su ba

Matashi dan shekara 37 ya kashe mahaifinsa dan shekara 70 a jahar Anambra
Matashi dan shekara 37 ya kashe mahaifinsa dan shekara 70 a jahar Anambra
Asali: UGC

Jami’i mai magana da yawun rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Anambra, Haruna Mohammed ya bayyana cewa sun kama mutumin, amma da alama yana da tabin hankali.

“A yau da misalin karfe 9:45 na safe wani mutumi mai suna Timothy Ezeofor dake kauyen Umuezegoro Umuchiana ya kai kara ofishin Yansanda inda ya shaida musu cewa da misalin karfe 8 na safiyar ranar aka kashe yayansa mai shekaru 70 a duniya, Godwin Ezeofor.

“Kuma dan sa mai shekaru 37 Chigorom Ezeofor ne ya kashe shi da hannunsa ta hanyar amfani da gatari. Bayan samun rahoton, sai DPO na Yansandan yankin Aguata, Ayeni Oluwadare ya jagoranci tawagar Yansanda zuwa inda lamarin ya faru.

“Sun dauki hotunan mamacin, sa’annan suka garzaya da shi zuwa asibiti, inda a can ne likitoci suka tabbatar da mutuwarsa, sa’annan aka mika gawarsa zuwa dakin ajiyan gawarwaki na asibitin domin gudanar da bincike.” Inji shi.

Daga karshe Haruna yace sun gano makamin da yaron ya yi amfani da shi wajen kashe baban nasa, kuma sun kama shi, a yanzu suna gudanar da bincike a kan sa.

A wani labari kuma, shugaba Muhammadu Buhari ya jajanta ma shugaban hukumar tsaro na DSS, Yusuf Magaji Bichi biyo bayan rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Kareematu Abubakar Bichi.

Shugaban ya mika sakon ta’aziyyar ne ta bakin babban hadiminsa na musamman a bangaren watsa labaru da kafafen sadarwar, Malam Garba Shehu a ranar Lahadi, 26 ga watan Afrilu.

A sakon jaje da taya alhinin, shugaban ya bayyana marigayiya Hajiya Kareematu wanda ta rasu tana da shekaru 96 a duniya a matsayin mutuniyar kirki wanda maye gurbin ta zai yi wuya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel