Masarautar Saudiyya ta soke hukuncin kisa ga kananan yara

Masarautar Saudiyya ta soke hukuncin kisa ga kananan yara

Gwamnatin kasar Saudiyya ta sanar da yin fatali da dokar hukuncin kisa a cikin dokokin hukunce hukuncen ta, amma ga wadanda suka aikata manyan laifuka yan kasa da shekara 18.

Daily Nigerian ta ruwaito shugaban wata hukumar kare hakkin yan adam na kasar Saudiyya, Awwad Alawwad ya bayyana sabon dokar a matsayin abin maraba da farin ciki.

KU KARANTA: Da dumi dumi: An sallami mutane 10 da suka warke daga cutar Coronavirus a Legas

Awwad yace dokar ta shafi duk wani da ya aikata babban laifi a lokacin da shekarunsa basu haura shekara 18 ba, ire iren wadannan ne hukuncin kisa ya sauka daga wuyansu.

Masarautar Saudiyya ta soke hukuncin kisa ga kanaan yara
Masarautar Saudiyya ta soke hukuncin kisa ga kanaan yara
Asali: Facebook

“Wannan rana ce mai matukar muhimmanci a wajenmu, kuma mun san cewa Sarkin Saudiyya dake kula da manyan Masallatai masu tsarki tare da yarima mai jiran gado, Yarima Muhammad Salman ne suka tabbatar da samuwar haka.

“Dokar za ta taimaka mana wajen samar da sabon kundin hukunta manyan laifuka, kuma ya tabbatar da manufar masarautar na gudanar da sauye sauye a dukkanin fannonin kasar don cika burin bukatar shekarar 2030 dake karkashin jagorancin Yarima Muhammad.” Inji shi.

Awwad ya bayyana cewa masarautar ta sanar da sauyin ne kwana daya bayan ta soke hukuncin bulala ga masu laifi a kasar.

Awwada ya sake nanata cewa hakan wata manuniya ce ga kokari da kuma kudurin kare hakkin dan Adam da kasar ta ke yi.

“Wannan doka na nufin duk wanda aka yanke ma hukuncin kisa dangane da wani laifi da ya aikata tun bai yi shekaru 18 ba an dauke masa hukuncin, sai dai kawai za’a yanke masa hukuncin zaman gidan yari da bai wuce shekara 10 ba.

“Muna da yakinin kasar Saudi Arabia za ta cigaba da inganta rayuwar jama’anta a kokarin ta na cimma muradan shekarar 2030 a karkashin jagorancin Sarkin Saudiyya dake kula da manyan Masallatai masu tsarki tare da yarima mai jiran gado, Yarima Muhammad Salman.” Inji shi.

Daga karshe Awwad ya jinjina ma gwamnatin na daukan wannan mataki a daidai lokacin da take yaki da yaduwar annobar Coronavirus a kasar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel