Gwamnatin El-Rufai ta kara wa’adin zaman gida da kwana 30, an wajabta rufe fuska

Gwamnatin El-Rufai ta kara wa’adin zaman gida da kwana 30, an wajabta rufe fuska

Gwamnatin jihar Kaduna a karkashin Nasir El-Rufai ta tsawaita wa’adin takunkumin kulle. Gwamnan ya sanar da cewa mutane za su cigaba da zaman gida na tsawon kwanaki 30.

Mai girma gwamna Malam Nasir El-Rufai ya bayyana cewa ya amince da shawarwarin da kwamitin da ke yaki da annobar cutar COVID-19 a karkashin Dr. Hadiza Balarabe ta kawo.

Ga jerin wadannan matakai:

1. Haramta fita a ranar Talata

A baya mutane su na damar fita waje a ranakun Talata da Laraba a jihar Kaduna. Malam Nansir El-Rufai ya ce daga yanzu ranar Laraba ce kurum za ta zama ranar da mutane za su fita su shan iska.

2. Amfani da tsummar fuska

Gwamnatin jihar Kaduna ta wajabta amfani da tsummar kare fuska ga duk wanda zai bar gida. Haka zalika Nasir El-Rufai ya ce dokar tazara za ta cigaba da aiki domin gujewa cincirindo.

KU KARANTA: Matakin da Gwamnatin Tarayya ta dauka na rufe mutane ya zo da matsala

3. Wuraren ibada da gidajen biki da sauransu

Gwamnatin Kaduna ta ce har gobe babu maganar bude makarantu, dakunan ibada, wuraren biki, filayen wasanni, dakunan cin abinci, tashar mota da duk dai inda ake samun cinkoson jama’a.

4. Baki daga waje

Babu wanda gwamnatin Kaduna za ta bari ya shigo cikin jihar a wannan lokaci na annobar COVID-19. Za a hukunta wadanda su ka yi yunkurin shigowa jihar, har a karbe lasisin tukinsu.

5. Rage albashi

Masu ba gwamna shawara da manyan jami’an gwamnati za su rika bada wani kaso daga albashinsu haka masu karbar akalla N67, 000 domin a samu a biya kowane ma’aikacin jihar.

Wadanda aka halattawa zirga-zirga a jihar su ne ma’aikatan lafiya, masu kashe gobara, malaman wutan lantarki da ruwa. Sai kuma jami’an tsaro da direbobin manyan motocin man fetur.

Gwamna El-Rufai ya ce masu saida abinci da kayan magani su na da damar yawo a jihar Kaduna.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel