Azumi ya na taimakawa garkuwar jikin mutum – Babban Likita
A wannan shekarar, musulmai su na ganin wani irin azumi na watan Ramadana a tsakiyar annobar cutar Coronavirus. Wani likita ya yi magana game da tasirin azumi ga lafiya.
Musulman da ke da koshin lafiya kuma mazauna gida su kan yi azumi na tsawon kwanaki 29 ko 30 inda su ke aurcewa abinci ko shan wani abu a tsawon lokacin yinin watan Ramadan.
Bana abubuwa sun sake zani domin masallatan da aka saba ganinsu a bude cike da mutane su na ibada a irin wannan lokaci, za su kasance a rufe saboda annobar cutar nan ta COVID-19.
Masana kiwon lafiya sun yi magana game da tasirin azumi wajen kamuwa da cutar. Likitoci sun bayyana cewa azumi ya na da amfani ga lafiyar jikin mutum ta hanyoyi daban-daban.
Amir Khan ya yi rubutu a Aljazeera ya ce cikin amfanin azumi shi ne taimakawa wajen karfafa garkuwar jikin mutum. Wannan ya sa wasu mabiya addinan su ka rungumi azumi.
KU KARANTA: Kano ta sake rasa wani Bajimin Shehin Malami a cikin sa'a 24
Azumi ya kan hana kumburin gabobin jikin mutum. Wannan ya na da amfani wajen kara lafiyar garkuwar jiki. Wadannan garkuwa su ne su ke kare mutane daga kamuwa da cututtuka.
Bincike ya nuna mutanen da aka yi a kasar Masar a shekarun baya sun rika yin azumi na tsawon lokaci domin fitar da cututtuka daga cikin jikinsu, wanda wannan ya nuna fa’idar azumi.
Rahoton ya bayyana cewa azumi ya na tada tsofaffin kwayoyin halittar mutum. Saboda rashin samun kayan marmari, jiki ya kan farfado da wasu kwayoyin halittar da su ka ragargaje.
A dalilin farfado da wadannan tsofaffi da rubabbun kwayoyin halitta, bayan azumi mutum ya kan zama ya samu karin lafiyayyun kwayoyin jikin da ke taimaka wajen ba shi kariyar cuta.
Duk da bincike ya nuna jiki na shiga hadari idan aka dauki lokaci ba tare da an ci abinci ba, sai dai an gano kwayoyin jikin mutum kan zabura da zarar an yi buda baki inji Dr. Amir Khan.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng