Za mu kaddamar da wurin gwajin kwayar cutar COVID-19 inji Jami’ar BUK
Shugaban jam’ar Bayero da ke garin Kano watau BUK, Farfesa Muhammad Yahuza Bello ya bayyana irin shirin da makarantar ta ke yi wajen yaki da annobar Coronavirus a jihar.
Muhammad Yahuza Bello ya ce jami’arsu ta BUK za ta tada dakin gwajin COVID-19 a cikin makarantar wanda zai taimakawa gwamnati wajen kokarin ganin bayan wannan annoba.
Shugaban jami’ar, Farfesa Muhammad Yahuza Bello ya yi wannan jawabi ne a gidan gwamnatin jihar Kano. Yahuza Bello ya ce jami’ar ta samu izninin wannan aiki daga hukumar NCDC.
Daily Trust ta ce Yahuza Bello ya zanta ne da ‘yan jarida a ranar Asabar, 25 ga watan Afrilu, 2020. A halin yanzu akwai mutane 77 da aka tabbatar sun harbu da cutar COVID-19 a jihar Kano.
Jami’an hukumar NCDC masu takaita yaduwar cututtuka a Najeriya sun kawo ziyara zuwa wajen da ake yin wannan aiki, kuma sun yi na’am da yunkurin jami’ar bayan kewayen da su ka yi.
KU KARANTA: Masu saba dokar zaman gida a Kano za su gamu da hukuncin kotu
Ma’aikatan hukumar ta NCDC sun zagaya sun ga dakunan bincike da kuma kayan aikin da ke cikin cibiyar kula da cututtuka masu yaduwa na jami’ar kamar yadda jaridar ta bayyana.
Farfesan ya ce gwamnati ta basu damar soma gwajin kwayar cutar COVID-19, kuma ana sa ran nan da kwanaki goma wannan dakin gwaji da aka kashewa makudan kudi ya fara aiki.
“Mu na sa ran nan da mako guda zuwa kwana goma a bude dakin gwajin da zai iya yi wa mutane kimanin 180 aiki a rana guda, akasin mutum 40 da dakin da ake da shi ya ke dauka kullum.”
“An dauko na’urorin PRC da ake da su a wasu cibiyoyin jami'ar zuwa wannan cibiya. Za mu kashe Naira miliyan 50 wajen kafa wannan daki.” Farfesa Bello ya fadawa ‘yan jarida wannan.
Shugaban jami’ar ya ce da farko sun saye rigunan gwaji 1500 wanda za ayi aiki da su na tsawon kwanaki goma. Bello ya roki gwamnatin jihar Kano ta samar da rigunan aikin Likitoci.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng