'Yan sanda sun tarwatsa taron ma su zaman makoki a Kaduna

'Yan sanda sun tarwatsa taron ma su zaman makoki a Kaduna

Wasu jami’an yan sanda sun tarwatsa dandazon mutane da suka halarci zaman makokin wani matashi a jahar Kaduna.

An gudanar da zaman makokin ne a ranar Asabar a garin Maraban Rido da ke karamar hukumar Chikun na jahar.

Yayin da suke tarwatsa taron, jami’an tsaron sun kama mutane da dama kan karya dokar hana fita da gwamnatin jahar ta kafa.

Gwamnatin jahar ta haramta duk wani taro na jama’a, ciki harda na zaman makoki da bukukuwa a kokarinta na hana yaduwar Coronavirus a jahar.

'Yan sanda sun tarwatsa taron ma su zaman makoki a Kaduna

'Yan sanda sun tarwatsa taron ma su zaman makoki a Kaduna
Source: Twitter

Ta kuma yi umurnin rufe jahar a ranar 26 ga watan Maris, har sai baba ya gani.

Ciki harda hana zinga-zirga, da haramta tafiye-tafiye da taron jama’a.

An kama mutanen ne yayin da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida a Kaduna, Samuel Aruwan, ya fita rangadi a wasu yankunan jahar.

Aruwan, wanda ya samu rakiyan wasu shugabannin hukumomin tsaro, ya yi bayanin cewa sun fita rangadi ne don ganin yadda ake bin dokar da gwamnati ta saka."

KU KARANTA KUMA: Abba Kyari: Babu ruwan APC a wanda zai zama shugaban ma’aikatan Shugaban kasa na gaba - Issa-Onilu

Kwamishinan yan sandan jahar, Umar Muri, wanda ya kasance cikin tawagar gani da idon, ya yi magana da manema labarai.

Ya bayyana cewa zaman makokin ya sabawa umarnun gwamnati da ta hana taron jama’a.

A wani labarin kuma, mun ji cewa gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da samun karin mutum daya mai dauke da cutar Covid-19, kwamishinar lafiya ta jihar, Dr Amina Mohammed Baloni ta sanar.

A takardar da kwamishinar ta fitar a ranar Asabar, ta ce sabon kamun na cutar yana daya daga cikin wadanda suka yi mu'amala da wadanda suka kamu a makon da ya gabata.

Kamar yadda Baloni ta sanar, Gwamnan jihar Kaduna ya jinjinawa kokarin kwararrun jihar. Ya yi kira ga jama'a da masu ruwa da tsaki na jihar da su ci gaba da kokari tare da gujewa yaduwar cutar.

Kwamishinar ta ce jihar ta yi nasarar samar da dakin gwajin cutar amma mai zaman kansa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel