Gwamnonin Jihohi sun roki Shugaban kasa Buhari ya takaita takunkumin kulle

Gwamnonin Jihohi sun roki Shugaban kasa Buhari ya takaita takunkumin kulle

Jaridar Premium Times ta fitar da rahoto cewa gwamnonin jihohin Najeriya sun fito sun bukaci gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta takaita dokar kullen da ta sa a wasu yankuna.

Gwamnonin sun yi kira ga gwamnatin tarayya ta haramta zirga-zirga daga wata jiha zuwa wata, amma ta kyale mutane su rika yawo a cikin jihohinsu, muddin ba a jawo cinkoson jama’a.

Ganin wa’adin takunkumin da aka sa ya gabato, gwamnonin jihohin sun bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya farlanta amfani da tsummar rufe fuska ga masu shiga bainar jama'a.

Kamar yadda rahoton ya nuna, gwamnonin sun gabatar da wannan bukatu ne a wata takarda da su ka aikawa sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, a ranar 24 ga watan Afrilu, 2020.

Shugaban gwamnonin Najeriya kuma gwamnan jihar Ekiti, Dr. Kayode Fayemi ne ya sa hannu a wannan wasika. Gwamnan ya na magana ne a madadin kungiyar NGF ta gwamnonin kasar.

KU KARANTA: Sai an hada da addu'a a kan mace-macen da ake yi a Kano - Hadimin Buhari

Gwamnonin Jihohi sun roki Shugaban kasa Buhari ya takaita takunkumin kulle
Shugaban kasa Buhari ya hana fita a Jihohin Legas da Ogun da Abuja
Asali: Twitter

Kayode Fayemi ya bayyana cewa sun cin ma wannan matsaya ne a sakamakon wani taro da su ka yi da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ta kafar yanar gizo a ranar Laraba.

Gwamnan gwamnonin ya shaida cewa Yemi Osinbajo ya bukaci jihohi su bada shawarar abin da su ke bukatar gwamnatin tarayya ta yi wajen maganin annobar Coronavirus da ta addabi kasar.

A ranar Litinin dinnan mai zuwa wa’adin dokar zaman gidan da gwamnatin tarayya ta sa zai zo karshe. Jaridar ta ce ba ta da masaniya ko shugaban kasar zai yi na’am da bukatun gwamnonin.

Kawo yanzu dai masana tattalin arziki da kungiyar NLC sun bukaci shugaban kasa Buhari ya guji tsawaita wa’adin dokar zaman gida. Ana tunanin wannan zai yi wa tattalin arzikin kasar illa.

Fayemi ya ce su na so a ba masu sayen kayan gona da abinci da maganguna da man fetur damar yawo. Gwamnonin sun kuma bukaci a hana cinkoson jam’a tare da haramta fita a cikin dare.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel