Gwamnatin Jihar Kano ta kafa kotu domin hukunta masu sabawa dokar kulle

Gwamnatin Jihar Kano ta kafa kotu domin hukunta masu sabawa dokar kulle

A ranar Asabar, gwamnatin Kano a karkashin Abdullahi Umar Ganduje ta ce ta kammala shirin kafa wasu kotu na musamman a wurare daban-daban domin hukunta masu sabawa doka.

Mai girma Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bada umarnin cewa jama’a su zauna a cikin gidajensu a jihar Kano. Sai dai ana samun wadanda su ke yi wa dokar hukuma kunnen kashi a jihar.

Wannan ya sa gwamna Abdullahi Ganduje ya shaidawa jihar Kano a lokacin da ya zanta da ‘yan jarida cewa za a rika hukunta masu sabawa dokar kullen domin a kare lafiyar Bayin Allah.

Gwamnan ya bayyana cewa batun rufe iyakokin jihar da aka yi ya na nan. Ganduje ya ce gwamnonin Arewa sun yarda su rufe iyakokinsu na makonni biyu a hana yaduwar cutar.

Ganduje ya yarda abubuwa su na neman su sukurkucewa jihar Kano a daidai wannan lokacin annoba. Duk da haka gwamnan ya ce su na bakin kokarinsu na takaita lamarin a Kano.

KU KARANTA: COVID-19 ta saki Gwamnan Kaduna bayan wata guda da harbinsa

Gwamnatin Jihar Kano ta kafa kotu domin hukunta masu sabawa dokar kulle
Gwamnatin Abdullahi Ganduje ta kafa kotu domin hukunta marasa zama a gida
Asali: Twitter

Gwamnatin Kano ta yi hayar wurin ajiye jinin wadanda za ayi wa gwaji. Bayan haka gwamnan ya ce dakin killace mutanen da ke filin wasan Sani Abacha zai iya daukar mutane 210.

Ganin irin kalubalen da ake fuskanta a Kano, Alhaji Aliko Dangote ya yi alkawarin bada gudumuwar rigunan aiki 5000 da kuma na’urar taimakawa numfashi inji Dr. Ganduje.

Bayan wannan kokari, gwamnatin Abdullahi Ganduje za ta soma rabon kayan tallafi ga mutane 50, 000 a jihar Kano. Gwamnan ya ce wannan agaji da za a bada zai ci fiye da miliyan 600.

Ganduje ya ce akwai asibitoci da wuraren killace masu wannan cuta da aka tanada. Bayan haka an dauke Almajirai sama da 1200 daga Kano an maida su ainihin jihohin da su ka fito.

Da ya ke jawabi a wajen taron, mataimakin gwamnan Kano kuma shugaban kwamitin yaki da cutar COVID-19 a jihar, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, ya yi kira ga mutanen Kano su bi doka.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel