Jihohi 6 da aka samu karin mutane 23 da annobar covid-19 ta harba

Jihohi 6 da aka samu karin mutane 23 da annobar covid-19 ta harba

A yayin da gwamnatin jihohi da tarayya ke cigaba da yaki da annobar covid-19 a fadin Najeriya, wasu jihohi guda 6 samu karuwar mutane 23 da suka kamu da kwayar cutar.

Jihohin sune; Ondo, Oyo, Osun, Zamfara, Kaduna da Nasarawa, kamar yadda kididdigar hukumar NCDC ta nuna.

A yayin da aka tabbatar da samun mutum na hudu da ke dauke da kwayar cutar a Ondo, gwamnan jihar ya zargi 'yan sanda da gaza tsare iyakokin jihar yayin da jama'a ke kwararowa daga Legas.

Mutum na hudu da aka samu da kwayar cutar a jihar Ondo, wani dan sanda ne da aka gwada a jihar Legas amma ya kasa zaman jiran sanin sakamakon gwajin da aka yi masa.

Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya tabbatar da cewa an mayar da dan sandan cibiyar killacewa da ke Akure, babban birnin jiha.

Gwamnatin jihar Osun ta bayyana cewa ta gudanar kwayar cutar covid-19 a kan mutane 167, wanda daga cikinsu aka tabbatar da samun kwayar cutar a jikin mutane 12.

A cewar kwamishinan lafiya na Osun, Dakta Rafiu Isamotu, mutanen 12 daka samu da kwayar cutar sun fito ne daga Osogbo, Ife, Ede, Ikire da Ejigbo da ke jihar.

Jihohi 6 da aka samu karin mutane 23 da annobar covid-19 ta harba
Jihohi 6 da aka samu karin mutane 23 da annobar covid-19 ta harba
Asali: Twitter

Da yammacin ranar Asabar ne gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi, ya bayyana cewa an samu karin sabbin mutane 4 da annobar covid-19 ta harba a jihar.

Kazalika, gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, ya sanar, a ranar Asabar, cewa rahoton hukumar NCDC ya tabbatar da cewa an samu mutum biyu da ke dauke da kwayar cutar covid-19 a jiharsa.

A jawabin da ya gabatar ga jama'ar Zamfara, gwamna Matawalle ya bukaci mazauna jihar su yi biyayya ga duk matakan da aka gindaya domin dakile yaduwar annobar a tsakanin jama'a.

DUBA WANNAN: Jerin sunayen fitattun mutane 16 da suka mutu a cikin sa'o'i 24 a Kano

Daga garin Pada da ke karamar hukumar Guruku a jihar Nasarawa, an samu a kalla mutane uku da annobar covid-19 ta harba.

Mataimakin gwamnan jihar Nasarawa, Dakta Emmanuel Akabe, ya tabbatar da hakan ga manema labarai ranar Asabar a garin Lafia, babban birnin jiha.

Kwamishinar lafiya ta jihar Kaduna, Amina Mohammed Baloni, ta bayyana damuwarta a kan sake samun mai dauke da kwayar cutar a Kaduna.

A cikim wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar, ta bayyana cewa ya zuwa ranar Asabar, adadin ma su dauke da kwayar cutar a jihar ya zama mutum hudu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel