An kama mai cutar coronavirus da ya tsere a jahar Borno

An kama mai cutar coronavirus da ya tsere a jahar Borno

- Gwamnatin Borno ta kama wani mai cutar COVID-19 da ya lallaba ya shige sansanin yan gudun hijira a jahar

- Mai cutar COVID-19 din shine ya jagoranci binne wanda aka samu da cutar na farko a jahar

- A bisa ga rahoto, sakamakon gwaji ya nuna yana da cutar bayan binne mutumin na farko

Gwamnatin Borno ta sanar da kama wani mutum da ke dauke da coronavirus, bayan ya jagoranci binne mutum na farko da ya kamu da cutar a jahar.

Wakilin Legit.ng a Borno, Inusa Ndahi, ya ruwaito cewa mara lafiyan ya yi nasarar tserewa sannan ya lallaba ya shige sansanin yan gudun hijira da ke Bakassi a Maiduguri, inda ya yi mu’amala da iyalansa da yan uwa.

Kwamishinan lafiya na jahar wanda ya kasance mamba a kwamitin kula da hana yaduwar COVID-19 a jahar, Salisu Kwayabura ne ya bayyana hakan a ranar Asabar, 25 ga watan Afrilu.

Ya bayyana hakan ne a jawabin manema labarai da ake gudanarwa a kullun a kan cutar ta corona, a gidan gwamnatin jahar.

An kama mai cutar coronavirus da ya tsere a jahar Borno
An kama mai cutar coronavirus da ya tsere a jahar Borno
Asali: Twitter

Ya bayyana cewa bayan sun samu labari kan inda mara lafiyan ya ke, sai kwamitin ya je sansasanin Bakassi inda suka dauke mutumin zuwa cibiyar killace masu cutar.

Ya kuma bayyana cewa a yanzu mutumin yana samun kulawar likitoci ba tare da ya nuna kowani alama na cutar ba.

Har ila yau kwamishinan ya ce gwamnan jahar, Babagana Zulum, ya yi umurnin sassauta rufe jahar da aka yi a ranakun Litinin, 27 ga watan Afrilu da Alhamis, 30 ga watan Afrilu.

A cewarsa hakan zai ba al’umman jahar damar sake siyayyan kayayyakin amfani.

Ya kuma ba da tabbacin cewa kwamitin zai samar da takunkumin fuska, abun kashe kwayoyin cuta na hannu ya mutane.

A wani laari makam,ancin haka, mun ji cewa wani mutum mai matsakaicin shekaru mai suna Johnbosco Ejiogu da ke Umudagu Mbieri a karamar hukumar Mbaitoli ta jihar Imo ya shiga hannun 'yan sanda.

Ana zargin mutumin ne da yunkurin kashe mahaifiyarsa mai suna Pauline Ejiogu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng