Magoya bayan Buhari sun bayyana wanda su ke so ya maye gurbin marigayi Abba Kyari

Magoya bayan Buhari sun bayyana wanda su ke so ya maye gurbin marigayi Abba Kyari

Gamayyar wasu kungiyoyin goyon bayan shugaban kasa, Muhammadu Buhari, sun yi kira gare shi da ya nada Injiniya Kilani Mohammed a gurbin marigayi Abba Kyari, tsohon shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa.

Gamayyar kungiyoyin a karkashin inuwar PBS sun bayyana cewa akwai bukatar Buhari ya samu gogaggen dan siyasa da ya san aiki domin nada shi a gurbin da marigayi Kyari ya bari.

Kungiyoyin PBS sun yi wa Buhari nemanyakin zabe tun farkon shigowarsa siyasa a 2003. Sune su ka fara kirkiro salon kare kuri'un da aka jefawa Buhari a karkashin tsarin 'A kasa A tsare'.

A karshen makon jiya ne marigayi Abba Kyari ya mutu a wani asibiti da ke jihar Legas, inda aka kwantar da shi bayan an tabbatar da cewa ya na dauke da kwayar cutar covid-19.

Tun bayan mutuwarsa rahotanni su ka fara bayyana jerin wasu manyan 'yan arewa ma su kusanci da shugaban kasa da ke zawarcin kujerarsa.

Magoya bayan Buhari sun bayyana wanda su ke so ya maye gurbin marigayi Abba Kyari

Buhari da marigayi Abba Kyari
Source: UGC

Kungiyar PSB ta bayyana cewa nada Dakta Kailani zai kwantar da hankulan jama'a a yayin da ake jimamin rashin Kyari.

PSB ta ce Dakta Kailani ya rike mukamin shugaban kungiyar kare kuri'un Buhari ta 'A kasa A tsare, mai kula da bangaren watsa labarai na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa tare da rike sauran wasu manyan mukamai.

DUBA WANNAN: Covid-19: Kura-kurai 7 da 'yan Najeriya ke tafkawa wajen amfani da takunkumi

Hakan na kunshe ne cikin jawabin da Suleiman Yola, daya daga cikin shugabanni a kungiyar PSB, ya fitar ranar Asabar a Abuja.

A cikin sanarwar, Yola ya bayyana cewa, "duk da har yanzu ana alhinin mutuwar marigayi Kyari kuma rashinsa ya jawo tsayawar al'amura da dama a kasa, maye gurbinsa da mutumin da ya cacanta kamar Dakta Kailani, zai kwantar da hankulan jama'a."

Daga cikin wadanda ake saka ran shugaba Buhari zai maye gurbin marigayi Kyari da su akwai ministan ilimi, Malam Adamu Adamu, tsohon gwamnan jihar Legas; Buba Marwa, Babagana Kingibe da sauransu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel