Farfesa Ibrahim Ayagi ya mutu a Kano
Fitaccen masanin ilimin tattalin arziki, Farfesa Ibrahim Ayagi, ya mutu ranar Asabar a jihar Kano, kamar yadda jaridar 'The Nation' ta wallafa.
The Nation ta ce wani makusancin marigayin ne ya sanar da ita labarin mutuwar Farfesa Ayagi.
An haifi marigayi Ayagi a shekarar 1940 a jihar Kano, ya mutu yana da shekara 80 a duniya bayan ya sha fama da rashin lafiya.
An yi jana'izarsa bayan sallar La'asar a gidansa da ke kallon makarantar sakandiren Gwale a cikin garin Kano.
Jaridar 'solacebase' da ke Kano ta rawaito cewa Yassir Ramadan Gwale, makwabcin marigayin, ya tabbatar mata da labarin mutuwar Farfesa Ayagi.

Asali: Twitter
Marigayi Ayagi, wanda ake girmamawa saboda iliminsa a bangaren tattalin arziki, ya taba rike babban darektan bankin 'Continental Merchant Bank'.
DUBA WANNAN: Covid-19: Kura-kurai 7 da 'yan Najeriya ke tafkawa wajen amfani da takunkumi
Farfesa Ayagi ya taba rike kujerar kwamishinan cigaban tattalin arzikin jihar Kano daga shekarar 1975 zuwa 1978.
Kazalika, ya rike mukamin babban darektan gidauniyar jihar Kano (Kano Foundation) daga shekarar 1987 zuwa 1990.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng