Yanzu-yanzu: An sake samun mai cutar Covid-19 daya a Kaduna

Yanzu-yanzu: An sake samun mai cutar Covid-19 daya a Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da samun karin mutum daya mai dauke da cutar Covid-19, kwamishinar lafiya ta jihar, Dr Amina Mohammed Baloni ta sanar.

A takardar da kwamishinar ta fitar a ranar Asabar, ta ce sabon kamun na cutar yana daya daga cikin wadanda suka yi mu'amala da wadanda suka kamu a makon da ya gabata.

Baloni ta jaddada cewa, "ana ci gaba da zakulo wadanda suka yi mu'amala da mutane ukun da suka kamu a makon da ya gabata tare da yi musu gwajin cutar."

"Kwararru a fannin kiwon lafiya suna kula da mutum 4 na jihar. Suna karbar magani ne cibiyar kula da cututtuka masu yaduuwa da ke da a cibiyar killacewa. Muna musu fatan samun sauki," ta tabbatar.

Kwamishinar ta tunatar da cewa, "Masana kiwon lafiya na ma'aikatar lafiya sun yi nasarar bada kulawar da ta kai ga warkewar mutum 6 na farko da suka samu cutar a jihar.

"Mutum na farko da ya kamu da cutar a jihar shine Malam Nasir El-Rufai. An sallamesa a ranar 22 ga watan Afirilun 2020 bayan gwaji biyu sun tabbatar da warkewarsa.

Yanzu-yanzu: An sake samun mai cutar Covid-19 daya a Kaduna

Yanzu-yanzu: An sake samun mai cutar Covid-19 daya a Kaduna
Source: UGC

KU KARANTA: COVID-19: A karo na farko, an samu bullar Korona a Zamfara

"Mutane biyar da suka warke an fara sallamarsu ne daga ranar 14 ga watan Afirilun 2020," ta kara da cewa.

Kamar yadda Baloni ta sanar, Gwamnan jihar Kaduna ya jinjinawa kokarin kwararrun jihar. Ya yi kira ga jama'a da masu ruwa da tsaki na jihar da su ci gaba da kokari tare da gujewa yaduwar cutar.

Kwamishinar ta ce jihar ta yi nasarar samar da dakin gwajin cutar amma mai zaman kansa.

Hukumar kula da cututtuka masu yaduwa ta NCDC ta tantance tare da amincewa da dakin gwajin, jaridar The Nation ta tabbatar.

Ta jaddada cewa za a sake samar da wasu dakunan gwajin a jihar. Daya zai kasance a asibitin koyarwa na jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria sai kuma daya a asibitin Abdullahi Tsoho da ke Kaduna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel