Yadda dattijuwa ta sheka lahira bayan yin azumin wata biyu a jere

Yadda dattijuwa ta sheka lahira bayan yin azumin wata biyu a jere

- Wata mata wacce ba a bayyana sunanta ba mazauniyar Sapele a jihar Delta ta sheka lahira bayan ta yi azumin kwanaki 60 a jere

- Kamar yadda ganau ba jiyau ba suka tabbatar, sun ce matar, mijinta da danta sun kulle kansu a gida ne inda suke kokarin kammala azumin

- Kamar yadda wata majiya ta tabbatar, iyalan kan sha ruwa ne a wasu lokutan kalilan da suke wannan aikin na bauta

Wata mata wacce ba a bayyana sunanta ba mazauniyar Sapele da ke jihar Delta ta rasa rayuwarta bayan yin azumin wattani biyu a jere.

Ganau ba jiyau ba sun tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a kan titin MTN da ke Okirigwhere a Sapele.

An gano cewa matar, mijinta da dan ta sun kulle kansu a gidansu ne na watanni biyu don kokarin kammala azumin kwanaki 60 cif.

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, wani aminin iyalan ne ya fara azumin kafin daga bisani su bi ayari.

An gano cewa suna shan ruwa ne a lokutan da bukatar hakan ta tsananta a lokacin da suke wannan azumin.

Wata majiya ta sanar da jaridar The Punch cewa, a yayin da aka samu mahaifiyar ta rasu, dan ya rame tamkar ba zai kai ba.

A halin yanzu, mijin da dan an mika su asibiti don samun taimakon gaggawa.

Yadda dattijuwa ta sheka lahira bayan yin azumin wata biyu a jere
Yadda dattijuwa ta sheka lahira bayan yin azumin wata biyu a jere
Asali: Twitter

KU KARANTA: An kama mutumin da ya haike wa matarsa har ta mutu a Jigawa

Gawar matar kuwa an dauketa inda aka kaita ma'adanar gawawwaki.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Onome Onovwakpoyeya, ta kasa tabbatar da aukuwar lamarin ko musantawa.

Ta ce babu wannan rahoton a tattare da 'yan sandan a wannan lokacin.

Onovwakpoyeya ta ce za su fara bincike a kan lamarin don gano gaskiyar zancen.

A wani labari na daban, rundunar yan sanda na jihar Jigawa ta kama wani mutum da aka zargin ya yi matarsa fyade har sai da ta mutu a kauyen Kankaleru da ke karamar hukumar Ringim na jihar.

A sanarwar da ya fitar a ranar Jumaa, Mai magana da yawun rundunar a jihar, Abdu Jinjiri ya tabbatar wa Channels Television kama mutumin.

A cewar Jinjiri, wanda ake zargin, Alasan Audu ya aikata laifin ne bayan ta ki amincewa su yi kwanciya ta aure.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel