Covid-19: Gwamnan PDP zai mayar wa Buhari mota uku ta shinkafa da ya ba jiharsa tallafi

Covid-19: Gwamnan PDP zai mayar wa Buhari mota uku ta shinkafa da ya ba jiharsa tallafi

- Gwamnatin jihar Oyo ta bayyana cewa za ta mayar wa da gwamnatin tarayya mota uku ta shinkafa da ta bata don rabawa talakawa da mabukata

- Kamar yadda mataimaki na musamman ga Gwamna Seyi Makinde a kan ayyukan noma ya sanar, shinkafar lalatacciya ce

- Dr Debo Akande ya jaddada cewa za su mayar da shinkafar ne bayan sun kammala tantance ta don a halin yanzu sun gano tana dauke da kwari

Gwamnatin jihar Oyo a ranar Juma'a ta bayyana cewa za ta mayar wa da gwamnatin tarayya buhun shinkafa 1,800 wacce ta bata a matsayin tallafi don duk kwari sun ci shinkafar.

Gwamnatin jihar Oyo din ta karba manyan motoci uku shake da shinkafar da hukumar kwastam ta kasa ta kwace ne a ranar Litinin, jaridar The Punch ta wallafa.

Mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde a kan harkokin noma, Dr Debo Akande, ya yi bayanin cewa buhu 1,800 din da gwamnatin tarayya ta basu na shinkafa duk lalatattu ne.

Akande ya ce, "Mun amshi wadannan kayayyakin ne daga gwamnatin tarayya ta hannun ma'aikatar tallafi da jin kan 'yan kasa kuma mun adana su.

Covid-19: Gwamnan PDP zai mayar wa Buhari mota uku ta shinkafa da ya ba jiharsa tallafi

Covid-19: Gwamnan PDP zai mayar wa Buhari mota uku ta shinkafa da ya ba jiharsa tallafi
Source: Facebook

KU KARANTA: Kano: Ana ci gaba rasa rayuka duk da musantawar gwamnati

"A yayin duba kayayyakin ne muka gane cewa kwari sun lalata shinkafar.

"A saboda haka, mun kafa kwamitin da zai kara duba shinkafar don tabbacin abinda muka karba.

"Ba mu son samar da wata matsala a yayin shawo kan wata matsalar. Mun duba sosai kuma abinda muke gani kenan.

"Mun amince za mu mayar da kayan daga inda suka fito. Idan akwai wasu da za su iya maye gurbinsu, muna so a bamu."

Akande ya yi alkawarin cewa wannan ba zai kawo tsaiko ba wurin raba tallafin da gwamnatin jihar ta yi alkawari.

Ya kara da cewa, "Mun san cewa gwamnatin tarayya ta bada tallafin kayayyakin abinci daban-daban. Muna da shirin yin rabo cikin kwanakin nan kuma ba za mu fasa ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel