Covid-19: Wani mutum ya fadi ya mutu bayan sauka daga motar haya a Jos
- Jama'ar garin Jos sun fada tsananin alhini da tashin hankali bayan wani mutum ya fadi ya mutu bayan ya sauka daga motar haya
- Kamar yadda jaridar Daily Trust ta bayyana, an ga jama'a suna gudun ceton rai tare da kokarin nisantar gawar mamacin
- Mutumin ya taho ne daga garin Ibadan na jihar Oyo tare da matarsa dauke da kaji a hannu
Hankula sun tashi a garin Jos na jihar Filato bayan wani mutum da ya sauka daga motar haya da ta dauko shi daga garin Ibadan na jihar Oyo.
Wakilin jaridar Daily Trust, wanda ya ziyarci inda lamarin ya faru ya samu mutane na gudu ba-ji-gani tare da gujewa gawar.
Wani mai faci da ke wurin da abun ya faru ya tabbatar da cewa mutumin ya shiga garin ne tare da matarsa dauke da kaji.
Tuni dai jama'a suka killace matar mutumin kafin isowar hukuma.
Jami'an kiwon lafiya na Jos ta kudu, wadanda aka tuntuba a wurin da lamarin ya faru sun ki yin tsokaci a kan al'amarin.
Amma kuma na ga jami'an lafiyar na hana mutane isa wurin gawar.
DUBA WANNAN: Kasashe 10 da aka fi samun masu dauke da cutar COVID-19
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa jihar Filato ta samu mutum na farko mai dauke da cutar a jihar a ranar Alhamis.
An gano cewa wacce ke dauke da cutar ta shiga jihar ne daga garin Kano.
Gwamnatin jihar Filato ta tabbatar da bullar cutar Covid-19 a karo na farko.
Wacce ta kawo cutar jihar mace ce wacce ake zargin ta kwaso kwayar cutar daga jihar Kano inda ta kai ziyara duk da dokar hana zirga-zirgar da aka kafa a jihar.
"Eh, mun samu bullar cutar a karon farko a jihar Filato. An samu kwayar cutar ne daga jikin wata mata wacce ta dawo daga jihar Kano.
"Babu bukatar a tada hankali, a halin yanzu tana daya daga cibiyar killacewa ta jihar.
"Amma tambaya ta farko da za mu yi shine ta yaya har matar ta fita daga jihar Filato ta je Kano kuma ta dawo duk da iyakokinmu a rufe suke," wani likita ya sanar da jaridar SaharaReporters.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng