Jama’an kasar Makkah sun fuskanci girgizan kasa a daren da aka dauki Azumi

Jama’an kasar Makkah sun fuskanci girgizan kasa a daren da aka dauki Azumi

Wani dan girgizan kasa mai karfin degree 2.7 a ma’aunin Ritcher ya auku a yankin Qunfudah dake cikin yankin kasa mai tsarki, kasar Makkah.

Rahoton kamfanin dillancin labarun kasar Saudiyya, SPA ya tabbatar da haka, inda ya ce lamarin ya auku ne a daren Juma’a, gabanin Musulmai su dauki haramar azumin Ramadan.

KU KARANTA: Dubi wasu kasashe guda 15 a Duniya da ba’a samu bullar cutar COVID-19 ba

Sai da yake girgizan bai yi karfi ba, amma wasu mazauna garin sun ji shi, kamar yadda jaridar Saudi Gazette ta ruwaito.

Jama’an kasar Makkah sun fuskanci girgizan kasa a daren da aka dauki Azumi

Jama’an kasar Makkah sun fuskanci girgizan kasa a daren da aka dauki Azumi
Source: Facebook

Kakaakin hukumar Saudi Geological Survey, SGS, Tariq Ab Al-Khalil ya tabbatar da aukuwar girgizan kasan, amma yace ba wannan bane karo na farko da ake samun hakan ba.

“Koda yake ana daukan tsawon lokaci kafin samun irin haka, amma ana yawan samun motse motse a cikin kasa a yankin, irin wannan girgizan ba shi da tasiri saboda ba shi da karfi, jama’a kadan ne suke iya fahimtarsa.

“Hukumar SGS na kula tare da sa ido a duk wani girgizan kasa da aka samu a masarautar Saudiyya gaba daya, don haka muke sanar da jama’a su kwantar da hankulansu, kada su firgita.” Inji shi.

Daga karshe Tariq ya yi addu’ar Allah Ya kare kasar Saudiyya daga dukkan sharri.

A hannu guda gwamnatin kasar Saudiyya ta amince a gudanar da Sallar asham a Masallacin Makkah duk da umarnin da ta baiwa jama’a da su yi sallolinsu a cikin gidajensu.

Sai dai an gudanar da sallar ne ba tare da wasu jama’a da yawa ba, daga limami sai wasu yan mutane kalilan da suka hada sahu da bai wuce biyu ba.

Wannan ya faru ne sakamakon bullar cutar Coronavirus a kasar wanda a yanzu haka ta kama mutane 15,102, ta kashe 127 sa’annan mutane 2049 sun warke sarai.

A wani labari kuma, akwai wasu kasashe 15 da basu samu bullar Coronavirus a cikinsu ba, daga cikin wadannan kasashe akwai 2 a nahiyar Afika; Lesotho da Comoros.

Sauran su ne: Kiribati, Marshall Islands, Federated States of Micronesia, Nauru, Palau Samoa, Solomon Islands, Tajikistan, Tonga, Turkmenistan, Tuvalu, Vanuatu da Koriya ta Arewa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Online view pixel