Yanzu Yanzu: Allah ya yi wa na hannun daman Tinubu rasuwa

Yanzu Yanzu: Allah ya yi wa na hannun daman Tinubu rasuwa

- Amintaccen hadimin Bola Tinubu shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Lati Raheem ya rasu

- Kafin mutuwarsa, Lati ya kasance babban jami'in tsaron jigon na APC

- Ya mutu ne bayan fama da lalurar hawan jini da suga

Allah ya yi wa babban jami’in tsaron Bola Tinubu, shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Lati Raheem rasuwa.

Marigayin ya kasance hadimin da Tinubu ya fi aminta da shi, wani na kusa da shi ya bayyana wa manema labarai.

Na hannun daman Tinubun ya rasu ne a ranar Juma’a, 24 ga watan Afrilu, bayan ya yi fama da rashin lafiya, jaridar TheCable ta ruwaito.

Yanzu Yanzu: Allah ya yi wa na hannun daman Tinubu rasuwa
Yanzu Yanzu: Allah ya yi wa na hannun daman Tinubu rasuwa
Asali: Facebook

A cewar wata majiya, hadimin na Tinubu na da lalura ta hawan jini da suga.

“Ya yi dan gajeren rashin lafiya sannan aka kwantar da shi a asibiti. Yana da lalura ta hawan jini da suga. Ya mutu a safiyar ranar Juma’a,” cewar majiyar.

KU KARANTA KUMA: An bukaci masu azumi su ci abinci mai yawa lokacin sahur da buda baki saboda coronavirus

A wani labari na daban, mun ji cewa Mamman Daura, ya ce an bukaci Abba Kyari ya zama mataimakin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a shekarar 1999.

Kyari, wanda ya rasu sakamakon kamuwa da cutar coronavirus da yayi a ranar 18 ga watan Afirilun 2020, shine shugaban ma'aikatan fadar shugaba Buhari.

A ta'aziyyarsa da Daura ya yi, ya kwatanta Kyari da mutum mai matukar hazaka wanda ya kusan zama mataimakin shugaban kasa a 1999.

"Wannan lokacin ya yi daidai da lokacin da kasar nan ta koma mulkin damokaradiyya kuma Abba Kyari na daga cikin na gaba a karfafa Janar Obasanjo.

"Bayan bayyanar Obasanjo a matsayin dan takara a jam'iyyar PDP, wata kungiyar mata da matasa sun dinga rokon Obasanjo a kan ya dauka Abba Kyari a matsayin abokin takara.

"Bayan tsananin muhawara da ta biyo baya, Obasanjo ya dauka Alhaji Atiku Abubakar a matsayin abokin tafiyarsa," Daura yace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel