Annobar Coronavirus: Gwamnatin Ganduje na bibiyan mutane 259

Annobar Coronavirus: Gwamnatin Ganduje na bibiyan mutane 259

Jagoran tawagar yaki da COVID-19 a jahar Kano, Dr Tijjani a ranar Juma’a, ya bayyana cewa gwamnati na aikin bibiyan mutane 259 cikin 300 da suka yi mu’amala da mai cutar a jahar.

Dr Hussain ya bayyana hakan ne a wata hira da jaridar The Nation.

A cewarsa, “daya daga cikin hanyar dakile wannan lamari shine gano wadanda suka yi mu’amala da mai cutar.

“A yanzu haka, mun lissafo sama da mutane 300 kuma muna bibiyar 259.

“Muna bibiyar wadannan mutane ne imma ta lambobin waya ko kuma ziyartansu a gidajensu domin tabbatar da cewa bamu bar kowace kofa ba."

Annobar Coronavirus: Gwamnatin Ganduje na bibiyan mutane 259

Annobar Coronavirus: Gwamnatin Ganduje na bibiyan mutane 259
Source: Facebook

Dr Hussaini ya yi bayanin cewa “A wadannan yan kwanaki 13 da aka kwashe tun bayan da muka gano mutum na farko da ke da cutar, mun samu lamura 320 da ake zargi, wanda a ciki gwaji ya tabbatar da 73.

“Har ila yau, biyu daga cikin mutane 73 da aka tabbatar sun kasance ma’aikatan lafiya. Tun bayan barkewar wannan annoba, mun yi nasarar lura da fasinjoji 53 wadanda suka fito daga wuraren da COVID-19 ya bazu sosai.

“Mun kuma kwantar da 63 daga cikin mutane 73 da aka samu da cutar, sannan za a kwashi sauran zuwa cibiyar killace masu cutar.

"Kamar yadda muka samu labari, yayin da muka fuskanci kalubale a makon da ya gabata saboda jigonmu ya kamu da COVID-19, gwamnatin jahar ta yi gaggawan tayar da sabon tsari domin tabbatar da cewar tsarin bai durkushe ba.

“Mun sake tsari mai karfi sosai a yanzu. Don haka mutanen Kano su yi imanin cewa za a daidaita wannan annobar ba tare da bata lokaci ba.

“Za kuma mu kafa tawaga da za su je su yi bincike, daukar samfuri da kuma tabbatar da kai wadannan samfurin wajen gwaje-gwajenmu.

KU KARANTA KUMA: Dalilan da suka sanya cutar Coronavirus ta ke ci gaba da yaduwa a Kano

“Muna tsarin kara yawan adadin mutanen da ke a tawagar daga 30 zuwa 40.

“Cibiyoyin gwaje -gwajenmu ba su samu karancin kayayyaki ba.”

Ya yi kira ga mutane da su ba gwamnatin jahar hadin kai a kokarinta na dakile cutar Coronavirus.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel