Abba Kyari: An nemi Buhari ya kacaccala mukamin shugaban ma’aikatan shugaban kasa

Abba Kyari: An nemi Buhari ya kacaccala mukamin shugaban ma’aikatan shugaban kasa

Masu kamun kafa a wajen shugaban kasa Muhammadu Buhari kan wanda zai maye gurbin Abba Kyari, suna kokarin ganin an kacaccala ofishin shugaban ma’aikatan shugaban kasar zuwa yanka biyu.

Hakan na zuwa ne gabannin nada sabon mutum da zai maye gurbin Mallam Kyari, wanda ya rasu a ranar Juma’a da ya gabata, bayan ya kamu da cutar Coronavirus.

Wadanda ke kokarin ganin an raba mukamin, sun bayar da shawarar samar da ofishin mataimakin shugaban ma’aikatan shugaban kasar.

Koda dai wasu tawaga sun nemi a shafe ofishin shugaban ma’aikatan shugaban kasar, mafi akasarin yan fadar shugaban kasar sun nemi a riki kujerar.

Abba Kyari: An nemi Buhari ya kacaccala mukamin shugaban ma’aikatan shugaban kasa
Abba Kyari: An nemi Buhari ya kacaccala mukamin shugaban ma’aikatan shugaban kasa
Asali: Twitter

An kuma tattaro cewa wasu daga cikin masu kamun kafar sun tsayar da tsohon gwamnan jahar Nasarawa, Umaru Tanko Almakura wanda ya ke a matsayin sanata mai ci a yanzu.

Da kuma Mallam Mahmud Ahmed Yayale, wanda ya kasance tsohon shugaban ma’aikatan tarayya, a matsayin wadanda suke so su maye gurbin marigayi Kyari.

An tattaro cewa shugaba Buhari na tattaunawa kan zabin da aka gabatar masa.

Bincike ya nuna cewa tarin ayyukan da ake bai wa CoS sun yi yawa kuma suna kawo matsaloli na rashin lafiya, jaridar The Nation ta ruwaito.

An tattaro cewa wasu daga cikin masu kamun kafar na ganin tarin ayyukan da aka daura wa tsohon CoS ne ya kara tabarbarar da lamarin lafiyarsa, saboda yana aiki tamkar agogo.

Bincike ya kuma nuna cewa tarin aikin da ke wuyan CoS ya yi sanadiyar da mafi akasarin ma’aikatu da hukumomi ke da mukaddashin shugabanni.

Kimanin hukumomin tarayya 80 ne basu da ainahin shugabanni.

Wata majiya, wacce ta nemi a sakaya sunanta, ta ce: “Zabi uku ke ga shugaban kasa a yanzu, ci gaba da tsarin shugaban ma’aikatan shugaban kasa, samar da mataimakin shugaban ma’aikatan shugaban kasar ko kuma shafe ofishin baki daya.

“Dukkanin zabukan ba sabbin abu bane amma hakan ya danganta da shawarar shugaban kasar.

“Misali, lokacin da Manjo Janar Abdullahi Mohammed ya ke a matsayin shugaban ma’aikatan tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a tsakanin a 1999 da 2007, Ambasada Esan, ya kasance mataimakinsa.

“A nashi bangaren, marigayi Umaru Musa Yar’Adua ya shafe ofishin CoS a 2008 sannan ya daura hakkin kula da fadar shugaban kasar a tsakanin jami’an gwamnati da wani babban sakatare."

KU KARANTA KUMA: Wani Gwamna ya yi umurnin suburbudan duk mutumin da ya fito babu takunkumin fuska a jaharsa

Sai dai ba a san ko yaushe Buhari zai nada CoS dinsa ba, amma mutane da dama sun shiga tseren.

Sabbin mutane da aka nemi a nada sune Sanata Al-Makura da Yayale Ahmed.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel