Katsina: 'Yan sanda sun kashe gagararrun 'yan bindiga 2, sun cafke masu garkuwa da mutane 10

Katsina: 'Yan sanda sun kashe gagararrun 'yan bindiga 2, sun cafke masu garkuwa da mutane 10

- Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta halaka gagararrun 'yan bindiga biyu tare da damke wasu mutum 10 da ake zargi da garkuwa da mutane a kananan hukumomi biyar na jihar

- Kafin haduwar 'yan ta'addan da ajalinsu a ranar Alhamis, an tabbatar da cewa sune ke gallabar jama'ar kananan hukumomin Batsari, Faskari, Charanchi, Dutsinma tare da birnin Katsina

- Kamar yadda rundunar ta bayyana, sun damke wani mutum mai suna Sa'ad Yahaya wanda ya kai wa mahaifinsa farmaki yayin da yake bacci

Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta halaka gagararrun 'yan bindiga biyu tare da damke wasu mutum 10 da ake zargi da garkuwa da mutane a kananan hukumomi biyar na jihar.

Kafin haduwar 'yan ta'addan da ajalinsu a ranar Alhamis, an tabbatar da cewa sune ke gallabar jama'ar kananan hukumomin Batsari, Faskari, Charanchi, Dutsinma tare da birnin Katsina.

Kamar yadda gidan talabijin din Channels ya bayyana, Kakakin rundunar, SP Gambo Isah ya sanar da manema labarai cewa an samu bindiga kirar AK 47 guda daya.

Akwai harsasai charbi biyar, babur kirar Bajaj daya, layu da kuma tsabar kudi har N6,465 a tare da 'yan bindigar da aka kashe.

Kamar yadda rundunar ta bayyana, sun damke wani mutum mai suna Sa'ad Yahaya wanda ya kai wa mahaifinsa farmaki yayin da yake bacci.

Ya yi wa mahaifin fashin N435,000 a yayin da yake bacci.

Katsina: 'Yan sanda sun kashe gagararrun 'yan bindiga 2, sun cafke masu garkuwa da mutane 10

Katsina: 'Yan sanda sun kashe gagararrun 'yan bindiga 2, sun cafke masu garkuwa da mutane 10
Source: Twitter

KU KARANTA: Kano: Ganduje ya kaddamar da rabon tallafin abinci ga mabukata (Hotuna)

A wani labari na daban, wata budurwar 'yar sanda mai suna Lovender Elekwachi mai aiki a Eneka, wacce ke kula da cunkoson shataletalen Eneka ta rasu bayan abokin aikinta ya harbeta.

Elekwachi mai matsayin sajan ta rasu ne a ranar Alhamis bayan Sajan Bitrus Osaiah ya harbeta da bindiga.

Gidan talabijin din Channels ya ruwaito cewa, rundunar 'yan sandan jihar Ribas ta damke Osaiah tare da mika shi sashen binciken manyan laifuka na rundunar.

Kamar yadda takardar ta bayyana, Osaiah wanda ke aiki da kwamitin tabbatar da hana cunkoso na jihar Ribas na fuskantar bincike mai tsauri a sashen binciken manyan laifuka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel