Mahaifin tsohon gwamnan jihar Borno ya mutu

Mahaifin tsohon gwamnan jihar Borno ya mutu

Labari da dumin duminsa da ke shigowa kafar watsa labari ta Legit.ng na nuni da cewa Allah ya yiwa Galadiman masarautar Dikwa, Modu Sheriff, rasuwa ranar Alhamis.

Marigayi Modu Sheriff mahifine ga tsohon gwamna, Sanata Ali Modu Sheriff, wanda ya mulki jihar Borno daga shekarar 2003 zuwa 2011 a karkashin inuwar jam'iyyar ANPP.

A cikin wani sako da mataimaki na musamman ga shugaban kasa, Bashir Ahmad, ya wallafa a shafinsa na dandalin sada zumunta, ya bayyana cewa shugaba Buhari ya mika sakon ta'aziyyarsa ga gwamnatin jihar Borno.

Shugaba Buhari ya mika sakon ta'aziyya na musamman ga shehun Borno da daukacin al'ummar jihar Borno, kamar yadda kakakinsa, Garba Shehu, ya bayyana a cikin sakon da ya fitar.

Legit.ng ta fahimci cewa an yi jana'izar marigayin tare da binne shi bisa tsarin addinin Musulunci a jihar Borno.

A ranar laraba ne Legit.ng ta wallafa cewa Mahaifin Ahmed Idris, babban akanta na kasa, ya mutu a jihar Kano.

Sanarwar mutuwar na kunshe ne a cikin wani sako da Henshaw Ogubike, kakakin babban akanta na kasa, ya aika wa manema labarai ranar Laraba.

"Mu na ma su bakin cikin sanar da mutuwar Alhaji Idris Hussain, mahaifin Ahmed Idris, FCNA, babban akanta na kasa. Ya koma ga mahaliccinsa ranar Laraba da safe. Ya mutu ya na da shekaru 96 a duniya.

DUBA WANNAN: Covid-19: Gwamnan PDP ya bayar da umarnin yin bulala ga duk wanda aka gani babu takunkumi a jiharsa

"Dattijon ya mutu ne bayan ya sha fama da jinya.

"Marigayi Ahaji Idris Hussain dan kasuwa ne mai son taimakon ma su karamin karfi da marayu. Ya yi rayuwarsa a unguwar Daneji da ke karkashin karamar hukumar birnin Kano a jihar Kano.

"Ya mutu ya bar 'ya'ya da jikoki da tattaba kunne ma su yawa. Daga cikin 'ya'yansa akwai Alhaji Ahmed Idris, FCNA, babban akanta na kasa.

"An binne shi bisa tsarin addinin Musulunci a Kano.

"Mu na sanar da jama'a cewa ba za a yi zaman makoki ba saboda dokar nesanta da zama a gida da gwamnatin tarayya ta saka domin dakile yaduwar annobar cutar covid-19.

"Ga ma su son kai ziyarar ta'aziyya, za su iya aika sakon waya ko kuma su aika sakonsu ta dandalin sada zumunta. Allah ya ji kansa," a cewar sanarwar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel