Coronavirus: Abin da ya sa na bayar da asibitina – Kwankwaso

Coronavirus: Abin da ya sa na bayar da asibitina – Kwankwaso

Tsohon gwamnan jahar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, ya yi karin bayani kan dalilin da ya sa ya ba gwamnatin Abdullahi Ganduje gudunmuwar asibiti domin jinyar masu fama da cutar coronavirus.

Gwamna Ganduje dai ya kasance babban abokin adawar Sanata Kwankwaso tun bayan da suka raba jam'iyya sakamakon babbancin akidar siyasa.

A cewar Kwankwaso "an tanadi wannan gini ne saboda amfanin mambobinmu na Kwankwasiyya da ma duk wani dan jahar Kano.

"Amma kuma bayan kammala shi don mu shigo da kayan aiki, sai ga wannan annoba ta shigo. Shi ya sa mu ka sayo kayayyakin yaki da cutar coronavirus.

"Akwai ma wasu karin wurare, kamar dakunanmu na taro, da idan bukatar bayar da su ta taso, za mu bayar da su. Amma mu na fata Allah ya takaita," a cewarsa.

Coronavirus: Abin da ya sa na bayar da asibitina – Kwankwaso
Coronavirus: Abin da ya sa na bayar da asibitina – Kwankwaso
Asali: UGC

Tsohon gwamnan ya kuma yin karin haske a kan mahawarar da ake yi a kan gadajen karfe da aka tanada a asibitin, maimakon irin gadajen da ake amfani da su a asibitoci.

Ya ce: "Kayan da muka yi oda ba su iso ba. Tun dama chan wadannan gadajen suna cikin asibitin."

KU KARANTA KUMA: Abba Kyari: Tsoffin yan majalisa sun tsayar da Abba Ali a matsayin shugaban ma’aikatan Buhari na gaba

Sanata Kwankwaso ya ce ya bayar da asibitin ne har zuwa lokacin da za a ga bayan annobar covid-19, sashin Hausa na BBC ya ruwaito.

Sai dai, ya ce har yanzu kwamitin da ke yaki da annobar cutar COVID-19 a jihar Kano bai tabbatar da karbar asibitin ko akasin haka ba.

A wani labarin kuma, mun ji cewa Daraktan cibiyar nazarin cututtuka masu yaduwa na asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, Farfesa Isah Abubakar ya bayyana dalilin da yasa suka dakatar da gwajin Coronavirus a Kano.

Daily Trust ta ruwaito, Isah ya ce an dakatar da gwajin ne domin samun daman gudanar da wasu yan gyare gyare a cibiyar gwaje gwajen na COVID-19.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel