Gwamnati ta na lura da yaduwar COVID-19 a Kano, Osun, Oyo da Edo - Sani Aliyu

Gwamnati ta na lura da yaduwar COVID-19 a Kano, Osun, Oyo da Edo - Sani Aliyu

A halin yanzu an samu fiye da mutane 800 da su ka kamu da cutar COVID-19 a Najeriya. Jaridar Daily Trust ta ce gwamnatin tarayya ta na sa idanu game da halin da jihohi su ke ciki.

Jihar Kano ta na cikin inda idanun gwamnatin tarayya su ke kamar yadda mu ka samu labari. Sauran jihohin da gwamnatin Najeriya ta ke bibiya su ne Osun, Oyo da kuma jihar Edo.

Shugaban kwamitin da shugaban kasa ya kafa domin yaki da cutar COVID-19 a Najeriya, Dr. Sani Aliyu ya bayyana wannan a lokacin da kwamitin ya zanta da manema labarai a Abuja.

Sani Aliyu ya ke cewa: “Saboda an kara yawan wadanda ake yi wa gwajin cutar, akwai yiwuwar za mu cigaba da samun karuwar wadanda su ka kamu da wannan cuta a nan (Najeriya).”

“Mu na samun labari game da karuwar masu cutar, mu na sa ido sosai game da Kano, Osun, Oyo da kuma jihar Edo. Mu na la’akari da abin da ke faruwa a jihar Kano.” Inji Dr. Aliyu.

KU KARANTA: Halin da Kano ta ke ciki ya na damun Gwamnatin Tarayya

Kawo yanzu jihar Kano ce ta uku a wajen fama da masu cutar COVID-19 a Najeriya. Akwai akalla mutane 70 da su ka kamu da cutar zuwa ranar Laraba. Kuma babu wanda ya warke a jihar.

A cewar shugaban kwamitin na PTF, gwamnatin tarayya ta na tattaunawa da gwamnatin Kano domin ganin yadda za a shawo kan annobar. “Mu na tuntubar gwamnatin Jihar Kano.”

A cikin kwanaki uku an samu labarin mutuwar mutane 150 a Kano. Hukumomi da gwamnati sun sha alwashin yin bincike domin gano musababbin wannan mutuwa da ake yi a jihar.

A kan wannan gaba ne ministan yada labarai, Alhaji Lai Mohammed ya gargadi mutane su guji amfani da wani tsimi da ake tallatawa a Kano da sunan yana maganin cutar COVID-19.

A Osun akwai mutane 20 da su ka kamu da wannan muguwar cuta. A yau kuma aka ji labarin an samu wanda ya mutu a sanadiyyar COVID-19 a Oyo. A Edo akwai mutum 17 da ke jinya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel