Dalilan da suka sanya cutar Coronavirus ta ke ci gaba da yaduwa a Kano

Dalilan da suka sanya cutar Coronavirus ta ke ci gaba da yaduwa a Kano

A makon nan ne dai gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana damuwa matuka dangane da yadda cutar Coronavirus ke ci gaba da yaduwa a jihar Kano tamkar wutar daji.

Gwamnatin ta ce muddin ba a tashi an farga ba, to kuwa jihar Kano na iya kasancewa cibiyar cutar kamar yadda karamin ministan lafiya, Dr Olorunnibe Mamora ya bayyana.

Daya daga cikin 'yan kwamiti na musamman da gwamnatin tarayya ta kafa kan cutar corona a Najeriya, Dr Aliyu Sani, ya ce idan cutar ta ci gaba da bazuwa a Kano tamkar Arewacin Najeriya ya kamu ne.

Mun ji cewa yanzu an kai matakin da har an dakatar da gwajin gano masu cutar corona a Kano domin su kan su masu gwajin sun kamu da cutar kamar yadda Dr Sani ya bayyana.

Yana mai cewa asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano ya rufe dakin gwajin cutar domin su kansu masu gwajin an gano cutar ta harbe su.

Bayanai suna kara fitowa daga Kano dalilan da suka sa aka dakatar da gwajin cutar korona a Kano.

A Larabar makon nan da muke ciki, mun ji cewa an dakatar da gwajin gano wadanda cutar corona ta harba a sanadiyar rashin kayan aiki na aiwatar da gwajin.

Farfesa Sadiq Isah na kwamitin yaki da cutar corona a Kano, shi ne ya tabbatarwa manema labarai hakan da cewa dole ce ta sanya aka dakatar da gwajin don babu sinadaran da ake bukata domin ci gaba da gwajin.

Daga bisani kuma Farfesan ya shaidawa sashen Hausa na BBC cewa, an kai sinadaran gwaje-gwajen amma babu damar ci gaba da aiki a dakin gwajin har sai bayan kwanaki biyu.

Dalilin hakan kuwa shi ne an riga da yin feshin kashe kwayoyin cuta a dakin da sai bayan an dauki wani tsawon lokaci kana a shige sa.

Wannan shi ne babban dalilin da ya sanya gwamnan Kano Abdullahi Ganduje, ya nemi gwamnatin tarayya da ta share masa hawaye na fafutikar dakile yaduwar cutar a jiharsa.

KARANTA KUMA: China ta bai wa Najeriya tallafin N48m na yakar cutar Coronavirus

Ganduje ya nemi gwamnatin tarayya ta agazawa jihar Kano da tallafin Naira biliyan 15 domin samun damar ci gaba da yakar cutar corona a jihar.

Idan ba a manta ba a ranar 11 ga watan Afrilun 2020 ne ma'aikatar Lafiya a Kano ta sanar da bullar cutar karo na farko a jikin wani tsohon Kwamishinan jihar bayan dawowarsa daga Birtaniya.

Tun daga wannan lokaci an rika samun ci gaba ta fuskantar yawan adadin wadanda annobar ta harba.

Taskar bayanai ta Hukumar dakile yaduwar cututtuka a kasar NCDC ta sanar da cewa, adadin wadanda cutar corona ta harba sun kai 981 a duk fadin Najeriya.

Jadawalin jihohin da cutar ta bulla da NCDC ta fitar ya nuna Kano ce ta uku a yawan masu fama da cutar bayan Legas mai mutum 582 da Abuja babban birnin kasar inda ake da mutane 133.

Hakan na nufin adadin wadanda cutar ta harba a Kano ya kai mutum 73 cikin makonni biyu kacal tun bayan bullar cutar a jihar. Sai dai har yanzu mutum daya ne aka tabbatar cutar ta hallaka a jihar.

Daya daga cikin manyan dalilai da suka sanya cutar ta ke ci gaba da yaduwa a jihar Kano shi ne yawan mutane da kuma cunkusonsu musamman a wuraren da ke tara jama'a.

Akwai kuma dalilin rashin yarda da har yanzu wasu na ganin cewa babu cutar kawai kanzon kurege ne da farfaganda ake yadawa domin cimma wata manufa a duniya.

Rashin yiwa dokar kulle da'a ta hana fita da tilasta zaman gida wadda gwamnati ta shimfida ta yi tasiri wajen bazuwar cutar a jihar Kano.

A kwanakin nan mun ji cewa rundunar 'yan sanda ta cafke 'yan kwallon kafa 30 a birnin Kano da ke yawo unguwa-unguwa domin buga tamaula da sunan gasa duk da dokar da gwamnati ta gindaya.

Kakakin rundunar Abdullahi Haruna ya ce an kama matasan ne a yankin karamar Hukumar Dala da ke birnin Kano, inda suka je domin taka leda.

KARANTA KUMA: Ganduje ya sake sabunta nadin mukamin shugaban hukumar yaki da rashawa na Kano

A baya bayan nan ne dai aka yada wani bidiyo da ke nuna wani cincirindon matasa na kallon kwallo a wani makeken fili a cikin birnin Kano.

An tsegunta cewa yayin da jihar ta fara aiwatar da dokar kulle, matasan suka fito da gasar kwallon kafa da suka yi wa lakabi da Coronavirus Cup.

Haka kuma ana iya wassafa jinkirin da gwamnatin tayi na rufe iyakokinta da hana shiga jihar yayin da cutar ta bulla a jihohin da ke makwabtaka da ita irinsu Kaduna, Katsina da Bauchi.

Sai kuma jigo cikin dalilan da suka sanya likafar annobar Coronavirus ta ke ci gaba a Kano shi ne labarin da wani Likita a Kano ya bayar kan shafinsa na Facebook.

Likitan mai suna James King, a ranar Alhamis ta makon jiya, ya tona asirin yadda mutumin na farko wanda coronavirus ta harba ya yi sakacin shigar da cutar jihar.

Ba tare da bayyana sunan wanda ya kamu da cutar ba, King ya zayyana yadda mara lafiyar ya garzayo asibitinsu kuma aka gaggauta mika shi wurin da aka tanada domin killace wadanda ake zargi su na dauke da cutar.

A rahoton da jaridar The Punch ta ruwaito, Dr. King wanda mazauni ne a jihar Kano, ya bayyana irin rashin hadin kai da suka samu daga bangaren mai dauke da hatsabibiyar cutar ta covid-19.

Ya ce mutumin ya ki bayyana wuraren da ya shiga, bayan kuwa ya halarci taron jama'a da dama.

A cewarsa, mutumin ya ziyarci asibitinsu a ranar 10 ga watan Afrilu, inda ya yi korafin zazzabi, rashin kwari a jika, bushewar baki, da kuma rashin kwadayin abinci.

KARANTA KUMA: Tallafin gwamnati saboda Coronavirus: An nemi buhuna 42 na kayan abinci an rasa a jihar Neja

Ya ce, "ba mu sani ba ashe mutumin ya fita kasar waje inda ya biyo mota daga Abuja gabanin dawowarsa jihar Kano. A yayin da ya kamo hanya daga Abuja, ya kuma yada zango a Kaduna gabanin dawowarsa Kanon a ranar 25 ga watan Maris, 2020."

"Ya boye mana duk wuraren da ya shiga gabanin zuwansa Kano. Ya kuma boye mana cewa alamomin cutar covid-19 sun bayyana a kansa na daukewar numfashi da tari. Ya kuma boye mana cewa ya ziyarci asibitoci da dama bayan dawowarsa Kano"

"Bugu da kari, ya kuma boye mana cewa ashe an tura da samfurin jininsa zuwa ga hukumar dakile yaduwar cututtuka NCDC domin gwajin lafiyarsa gabanin ya gabatar mana da kansa."

King ya cigaba da cewa, "Abin da kawai mutumin yayi ikirari shi ne rashin jin dadin jikinsa na 'yan kwanaki kadan, ba tare da bayar da shaidar yana fuskantar numfashi da kyar, masassara da kuma tari."

"Bayan mun kammala duba shi ba tare da ya bamu duk wancan bayanai ba, mun ba shi gado a daya daga cikin dakunan marasa lafiya da misalin karfe 7.30 na yammacin ranar Juma'a 10 ga watan Afrilu."

"Ya yi cudanya da likitoci biyu da kuma masu taya likita aiki guda uku da kuma wani ma'aikacin mu guda daya."

"Mun kuma gano cewa a yayin da yake fama da rashin lafiya gabanin gabatar mana da kansa, ya halarci sallolin Juma'a, da sauran taro na jama'a,"

"Bayan wayewar gari, mahukunta lafiya sun garzayo asibitin da umarnin da gwamna ya basu na rufe asibitin baki daya."

"Sun dauke mara lafiyan zuwa wurin da gwamnatin Kano ta tanada a wajen gari domin killace wadanda ake zargin sun kamu da cutar coronavirus."

"Haka kuma an killace mu a cikin asibitinmu tare da daukar samfurin jinin mu domin aiwatar da gwajin covid-19."

"Bayan shafe kwanaki, ba mu da damar ganin iyalai ko 'yan uwanmu. Amma daga karshe sakamakon gwajin mu ya fito a ranar Laraba, 15 ga Afrilun 2020, kuma babu wanda cutar ta harba."

"Sai dai ya zuwa yanzu ba a bari mun fito daga inda aka killace mu ba." inji Dakta King

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel