Abba Kyari: Tsoffin yan majalisa sun tsayar da Abba Ali a matsayin shugaban ma’aikatan Buhari na gaba

Abba Kyari: Tsoffin yan majalisa sun tsayar da Abba Ali a matsayin shugaban ma’aikatan Buhari na gaba

- Kungiyar tsoffin yan majalisar dokoki a Najeriya sun bayyana mutumin da suke so ya maye gurbin Abba Kyari a matsayin shugaban ma’aikatan Buhari

- Tsoffin yan majalisan sun ce Sanata Abba Ali na da dukkanin abunda ake bukata wajen aiki a matsayin shugaban ma’aikatan shugaban kasa

- Kyari, marigayi shugaban ma’aikatan shugaban kasa, ya rasu ne a ranar Juma’a, 17 ga watan Afrilu, sakamakon cutar coronavirus, yan makonni bayan ya kamu da cutar

Kujerar shugaban ma’aikatan shugaban kasa Muhammadu Buhari ta na kasuwa, sakamakon mutuwar Abba Kyari wanda shine ke a kan kujerar har zuwa mutuwarsa a ranar Juma’a, 17 ga watan Afrilu, sakamakon COVID-19.

Ana ta jero sunayen manyan yan siyasa da dama a matsayin wadanda ake ganin Shugaba Buhari zai nada domin maye gurbin marigayi Abba Kyari.

Kungiyar tsoffin yan majalisa (LFP) su ma sun shiga cikin tattaunawar a ranar Laraba, 22 ga watan Afrilu, ta hanyar neman shugaban kasar ya nada Sanata Abba Ali.

Abba Kyari: Tsoffin yan majalisa sun tsayar da Abba Ali a matsayin shugaban ma’aikatan Buhari na gaba

Abba Kyari: Tsoffin yan majalisa sun tsayar da Abba Ali a matsayin shugaban ma’aikatan Buhari na gaba
Source: UGC

A cewar jaridar The Guardian, kungiyar LFP sun fada ma manema labarai a Owerri, babbar birnin jahar Imo, cewa Ali ne ya fi dacewa da wannan babban matsayi, kasancewarsa hazikin lauya kuma mai ilimi.

Legit.ng ta tattaro cewa tsohon mukaddashin gwamnan jahar Imo, Kelechi Iwuagu, Alhaji Gambo Sallau, AbdulAziz Gafasa da Kabiru Rurum a cikin wata takarda da suka sa hannu sun ba Shugaba Buhari tabbacin cewa zabinsu zai iya aikin da kuma yi wa yan Najeriya hidima.

KU KARANTA KUMA: Za a dauki lokaci mai tsawo ana fama da annobar coronavirus - WHO

Tsoffin yan majalisar sun jaddada cewa Ali na da dukkanin kyawawan halayya da Buhari ya bayyana na marigayi shugaban ma’aikatansa, inda suka bayyana shi a matsayin “dan Najeriya mara kabilanci.”

A wani labarin kuma, mun ji cewa Richard Kpodoh, wanda ya na daya daga cikin wadanda su ka kafa jam’iyyar APC mai mulki, ya sa baki game da wanda ya kamata ya zama sabon shugaban ma’aikatar fadar shugaban kasa.

Cif Richard Kpodoh ya ce Abdulrahaman Abdallah ya na cikin wadanda su ka fi kowa dacewa da rike mukamin na shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari.

Ganin irin cancantarsa ne Kpodoh ya roki shugaba Muhammadu Buhari ya nada Alhaji Abdulrahaman Abdallah a matsayin wanda zai maye gurbin da Abba Kyari ya bari a Aso Villa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel