Hukumar NCDC ta jinjinawa aikin da mu ke yi na yaki da COVID-19 inji Abiodun

Hukumar NCDC ta jinjinawa aikin da mu ke yi na yaki da COVID-19 inji Abiodun

Hukumar NCDC mai takaita yaduwar cutar COVID-19 a Najeriya da kuma kungiyar lafiya ta Duniya ta WHO sun yi magana game da matakin da wasu gwamnonin kasar nan ke dauka.

Wadannan manyan hukumomi sun yaba da irin abin da su ka ga gwamnatin jihar Ogun ta na yi domin hana yaduwar wannan mummunar cuta ta Coronavirus da ta zama annoba a Duniya.

NCDC da WHO sun ji dadin yadda su ka ga gwamnatin Dapo Abiodun ta tashi tsaye wajen ganin tayi yaki da wannan cuta a jihar Ogun. Hukumomin lafiyan sun ce abin da su ka gani ya burgesu.

Irin kayan aikin da aka zuba a kasa da kuma hobbasan gwamnatin Dapo Abiodun wajen kawo karshen COVID-19 ne ya jawowa jihar Ogun yabo daga hukumar NCDC da kungiyar WHO.

Wadannan manyan jami’ai masu kula da lafiya sun ce gwamnan ya tashi tsaye da nufin ganin jihar Ogun ba ta da annobar mafaka ba. A yanzu mutum 6 sun warke daga cutar a Ogun.

KU KARANTA: Gwamnoni sun yi na'am da garkame iyakoki domin hana zirga-zirga

Shugaban hukumar NCDC na kasa, ya yabawa gwamna Dapo Abiodun ne bayan da ya ziyarci wani dakin bincike da gwamnatin jihar ta kafa a asibitin koyarwan jami’ar Olabisi Onabanjo.

Haka zalika Dr. Chike Ihekweazu ya zagaya zuwa dakin jinyar da gwamnatin Ogun ta gina a garin Ikenne. Wannan katafaren daki ya na da gadaje 128 da za a iya kwantar da masu COVID-19.

Akwai wani wurin killace masu cutar COVID-19 da aka gina a garin Sagamu. Dr. Ihekweazu ya ce ya kamata sauran jihohi su yi koyi da salon gwamnan Ogun wajen yaki da annobar cutar.

Legit.ng Hausa ta samu labari daga shafin gwamnan na jihar Ogun cewa nan ba da dadewa za a kammala ginin dakin killace wadanda duk wannan cuta ta COVID-19 ta kama a Iberekodo.

Shugabar hukumar WHO ta Najeriya, Dr. Fiona Braka ta jinjinawa gwamnan. A cikin makon nan har wa yau, hukumar NCDC ta yabi kokarin da ta ga gwamna Seyi Makinde ya na yi a Oyo.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel